✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Ukraine: ’Yan Najeriya sun koka kan kai musu dauki a makare

’Yan Najeriya mazauna Ukraine sun koka kan yadda aka kai musu dauki bayan lokaci ya kure.

Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa za ta kwaso duk wani dan Najeriya da ke kasar Ukraine sakamakon hare-hare da kasar Rasha ta kaddamar.

Sanarwar na zuwa ne yayin da zaman zullumi ke karuwa kuma mutane ke neman mafaka saboda hare-haren na Rasha bayan mamayar da ta yi wa wasu yankunan Ukraine.

Wani dan Najeriya mazaunin birnin Kiev, Edidiong,  ya bayyana cewa, “A 2013 irin wannan rikicin ya taba faruwa kuma mahukunta Najeriya suka ce za su kwaso mu amma ba su cika alkawari ba.

“Muna bukatar addu’o’in ’yan Najeriya don a halin da ake ciki Ubangiji ne kadai Zai iya ceton mu.

“Ofishin Jakadancin Najeriya da ke nan ba su so a fadi gaskiya,” a cewarsa.

Ita ma Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta yi aiki tare da Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje don dawo da ’yan Najeriyar da ke zaune a Ukraine da Rasha.

Jama’a da dama sun shiga a birnin Belgorod na kasar Rasha wanda ke kusa da kan iyakar kasar Rasha da Ukraine.

An shiga halin zullumi saboda karar harbe-harben rokoki da Rasha ke harba wa Ukraine babu sassauci.

Tuni mutane suka kaurace wa tittunan birnin saboda fargabar abubuwan da ka iya faruwa.