✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Siyasa: ECOWAS ta kakaba wa Mali sabbin takunkumai

ECOWAS ta sanar da janye illahirin jakadun kasashen Yammacin Afirka daga kasar Mali.

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta sanya wa Mali sabbin takunkumai don tilasta wa sojoji gaggauta mika mulkin kasar a hannun zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya.

Wannan dai na cikin matakin da ECOWAS ta zartar a yayin taron shugabannin Kasashen Yankin Afirka da ya gudana a ranar Lahadi.

Sauran matakan da taron ECOWAS ya dauka sun hada da rufe iyakokin Mali da ilahirin kasashen da ke makwaftaka da ita.

Doriya a kan haka, taron na ECOWAS ya ce daga yanzu ba za a bai wa sojojin da ke mulki a Mali damar taba kudaden da kasar ta mallaka cikin asusun ajiyarta da ke Babban Bankin Kasashe masu amfani da kudin Cfa wato BECEAO ba, sai dai kudaden da za a yi amfani da su domin sayen magunguna ko kuma wasu abubuwa na bukatar gaggawa.

Har ila yau taron, wanda ya hada da kungiyoyi biyu, wato ECOWAS da kuma UEMOA, wato Kungiyar Kasashe Masu Amfani da Takardar Kudin Cfa, ya ce daga yanzu an haramta duk wata hada-hadar kudade tsakanin Mali da sauran kasashen yankin 14.

Domin nuna wa sojojin Mali cewa da gaske suke yi, kasashen na yammacin Afirka sun sanar da janye ilahirin jakadunsu daga kasar ta Mali.