✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin shugabancin UNILAG ya dauki sabon salo

Rikici ya kara kunno kai a Jami’ar Legas (UNILAG) bayan ta nada Farfesa Omololu Soyombo a matsayin shugabanta na riko a ranar da Majalisar Gudanarwarta…

Rikici ya kara kunno kai a Jami’ar Legas (UNILAG) bayan ta nada Farfesa Omololu Soyombo a matsayin shugabanta na riko a ranar da Majalisar Gudanarwarta ta sallami shugaban jami’ar, Farfesa Oluwatoyin Ogundipe.

Wani makusancin UNILAG ya shaida wa wakilinmu cewa Farfesa Soyombo zai rike mukamin har zuwa lokacin da za a nade sabon shugaban jami’ar.

A ranar Laraba ne Kwamitin Gudanarwan Jami’ar karkashin Dakta Wale Babalakin ta sanar da sallamar Farfesa Ogundipe nan take ne bisa zargin facaka da dukiyar jami’ar da sakaci da aiki.

Ra kuma nada Farfesa Soyombo a matsayin mukkadashin shugaban jami’ar.

— Sokiburutsu suke yi

Sai dai Farfesa Ogundipe ya yi fatali da sanarwar tsige shin da Rajistaran Jami’ar Oladejo Azeez ya fitar, yana mai cewa ‘sokiburutsun’ da kwamitin gudanarwan ya yi ya saba da dokokokin jam’iar.

Ya bukaci dukkan al’ummar jami’ar da su yi watsi da sanarwar domin shi ne halastaccen shugaban jami’ar saboda ‘ikirarin’ tsigewar da kwamitin Babalakin ya yi haramtacce ne.

Ita ma kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU reshen jam’iar ta yi watsi da tsige shi din, duk da cewa a baya ta sha zarginsa da aikata laifukan almundahana.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta nesanta sauke Farfesa Ogundipe daga mukaminsa, tana mai cewa ba a bi tsari ba wurin daukar matakin.

“Makarkashi ya ce da Babalakin ya shirya kuma babu dalilin yin haka”, inji sanarwar da Shugaban kungiyar Dele Ashiru ya fitar.

Ya kara da cewa, “Uban jami’an ya shirya hakan ne domin tayar da fitina a jami’a.

“Har yanzu muna goyon baya tare da nuna gamsuwarmu ga kamun ludayin shugabancin Farfesa Toyin Ogundipe”, inji shi.