Rikicin shugabanci ya kunno kai a kan kujerar shugabancin jam’iyar APC a matakin Jihar Katsina, inda nan gaba kadan ake shirin yin zaben shugabannin jam’iyar a matakin jiha.
Mutum biyu ne dai ke neman kujerar kuma kowannensu na takama da samun goyon bayan wani bangare na mukarraban gwamnatin jihar, musammam Gwamna Aminu Masari da Sakataren Gwamnatin Jihar, Mustafa Inuwa, wanda ake ganin zai fito takarar gwamnan a 2023.
Sabon rikicin dai dai ya fara bayyana ne a daren ranar Litinin inda Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Katsina, Shitu Maslaha, ya sa aka cire fastocin abokin hamayyarsa, Bala Abu Musawa, wanda shi ne mataimakinshi a shiyyar Funtuwa.
Wakilin Aminiya ya ziyarci ofishin jam’iyar don gane wa idonsa, inda ya samu matasan da aka sa su cire fastoccin suna tsaka da aikin, bisa umarnin shugaban jam’iyar kuma mai neman sake komawa bisa wannan mukami, Shitu Maslaha.
A cewar Maslaha, yanzu ba lokacin lika fastar siyasa ba ce, duk kuwa da cewa takarar kujerar shugabancin jam’iyya ce ba na mukamin gwamnati ba.
Usman Musa Liba wanda ake kira da Sarkin Aleru shi ne wanda ya yi magana a madadin matasan da aka sanya suka yi aikin cire fastocin, ya ce da ma ofis din ya zamo daga su sai aljannu ke zama a cikinshi, domin babu wani daga cikin shugabannin jam’iyar da ke zuwa balle ya san halin da ake ciki har ma a ba su wata kulawa.
Da aka tuntube shi a kan lamarin, Bala Abu Musawa ya ce, “In an cire fastocina a ofis ai ba za a cire ni a cikin zukatan jama’a ba”, inda ya kara yi kira ga magobayanshi da kada su tayar da hankali domin siyasa ta gaji irin haka.
Har dai zuwa kammala wannan rahoto, mun yi kokarin jin ta bakin shugaban jam’iyar wanda aka ce shi ne ya bayar da wancan umarni, amma ba mu same shi ba, mun yi ta kiran wayarsa amma ana cewa tana rufe.