✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin kabilanci: Gwamnatin Gombe ta sanya dokar hana fita

An sanya dokar hana fita ta awa 24 bayan rikicin tsakanin kabilun Waja da Lunguda a Jihar Gombe

An sanya dokar hana fita na awa 24 a bayan barkewar rikicin kabilanci a garuruwan Nyuwar da Jessu da Yolde na Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.

Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya dokar ne bayan kabilun Waja da Lunguda a garuruwan sun ba wa hamata iska, tare da asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa tun da saniyn safiyar Talata.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya sanar da kafa dokar a cikin wata takarda, wadda Babban Daraktan Labarai na Gwamnan Jihar, Isma’ila Uba Misilli, ya rattaba wa hannu.

Rikicin ta lakume dukuyoyi masu tarin yawa. Hoto: Rabilu Abubakar.

Farfesa Njodi yace sanya dokar hana fitar ta zama dole domin a tabbatar da kwanciyar hankali.

Ya kara da cewa tuni aka tura jami’an tsaro zuwa yankunan domin tabbatar da doka da oda.

Zuwa lokacin kammala wanann rahoto, babu cikakken bayanin gani da adadin wadanda abin ya ritsa da su ko yawan asarar da aka yi a rikicin.