✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin APC: Ko sulhu tsakanin bangaren Shekarau da na Ganduje zai yiwu?

Bangaren Shekerau ke daukar Danago a matsyain shugaban jam’iyyar, bangaren Ganduje yana daukar Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar.

Amakon jiya ne aka fara wani sabon zaman sulhu don neman bakin zaren rikicin cikin-gida da ya dabaibaiye Jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Rikicin ya samo asali ne kan shugabancin jam’iyyar a tsakanin bangaren Sanatan Kano ta Tsakiya kuma tsohon Gwamnan Jihar Malam Ibrahim Shekarau da bangaren Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

Yayin da bangaren Sanata Ibrahim Shekerau ke daukar Alhaji Ahmadu Haruna Zago a matsyain shugaban jam’iyyar, bangaren Gwamna Ganduje yana daukar Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar.

An gudanar da zaman sulhun ne a karkashin jagorancin Shugaban Riko na Jam’iyyar APC ta Kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai mala Buni da Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar da tsohon Shugaban Majlaisar Wakilai Mista Yakubu Dogara.

A lokacin zaman Sanata Kabiru Gaya ne ya wakilci bangaren Gwamna Ganduje shi kuma Sanata Ibrahim Shekarau ya wakilci bangarensa.

Majiyar Aminiya ta ce bayan jawaban da aka gabatar na neman daidaitawa tare da alkawarin yin adalci ga kowa dukkan bangarorin biyu sun amshi tayin uwar jam’iyyar na ajiye makamansu a rungumi tsintsiya wato a dunkule wuri guda.

Majiyar ta kara da cewa sai dai akwai batutuwan da suke da sarkakiya wadanda suka sa ba a iya kare sulhun a lokaci guda ba. Misali dambarwar shugabancin jam’iyyar wanda yanzu haka yake gaban kotu da kuma jerin bukatun da kowane banagre ke rokon ganin ya rabauta da su a zaman sulhun.

Bayan tattaunawar Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa a shirye bangarensa yake ya yi sulhu da daya bangaren “Allah ne da kanSa Ya ce sulhu alheri ne, don haka a shirye muke mu karbi tsarin sulhu,” inji shi.

Sai dai ya ce yin sulhun zai tabbata ne bisa wasu sharudda da za su gindaya.

A cewar Malam Shekarau suna yin wanann gwagwarmaya ce don tabbatar da adalci a shugabancin jam’iyya. “Babban burimu shi ne tabbatar da gaskiya da adalci wajen samar da tsarin shugabanci a Jam’iyyar APC. Muna tabbatar wa al’ummar Jihar Kano cewa wannan gwagwarmaya da muke yi ba ta nufin cin mutunci ga kowa ko tozarta wani,” inji shi.

Mai magana da yawun bangaren Gwamna Ganduje Ahmd S. Aruwa ya ce suna nan a kan bakarsu cewa har yanzu Abdullahi Abbas ne Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Idan za a iya tunawa a ranar 14 ga Satumban bara, shugabannin Jam’iyyar APC sun kafa wani kwamiti mai mutum tara a karkashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Nassarawa Sanata Abdullahi Adamu domin sulhunta ’ya’yan jam’iyyar da suka samu rabuwar kai a dukkan jihohin kasar nan.

To amma a ranar 13 ga watan Oktoban da ya gabata sanatocin Kano uku da suka hada da Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Kabiru Gaya da Sanata Barau Jibrin da wadansu ’yan Majalisar Wakilai hudu da wadansu ’ya’yan jam’iyyar suka aike wa uwar jam’iyyar korafin rashin amincewa da tsarin da Gwamna Ganduje da mukarrabansa ke tafiyarwa a Kano. Sai dai awanni kadan bayan wannan Sanata Kabiru Gaya ya fice daga wancan ayari.

A ranar Litinin 29 ga Nuwamban bara, kwamitin Sanata Adamu Abdullahi ya fara aikinsa da Jihar Kano, inda ya fara zama da bangaren Sanata Ibrahim Shekarau a otel din Tahir daga baya kuma ya gana da bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje, sannan daga bisani aka zauna da dukkan bangarorin a lokaci guda a fadar Gwamnatin Jihar Kano.

Wannan zama ya samu halartar Gwamna Abdullahi Ganduje da Mataimakinsa Dokta Nasiru Yusuf Gawuna da Sanata Kabiru Gaya da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhaji Alhassan Ado Doguwa da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma wani dattijon jam’iyyar, Alhaji Nasiru Aliko Koki.

A daya bangaren kuma akwai Sanata Ibrahim Shekarau da Farfesa Hafiz Abubakar da Alhaji Aliko Muktar da Dokta Mustapha Musa da Injiniya Sarki Labaran da Barista Habibu Kankarofi.

An shafe tsawon awanni, inda aka kwana ana tattaunawa amma ba a kai ga cimma matsaya ba.

Haka wancan kwamiti ya koma Abuja, inda wutar rikicin cikin gida ta ci gaba da ruruwa a jihar.

Abin jira a gani a yanzu shi ne ko wannan yunkurin sulhu a zagaye na biyu zai yi nasara?