✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikici ya barke tsakanin masu bore kan sakamakon zabe a Abuja

An samu rabuwar kai tsakanin bagarorin masu zanga-zanga kan sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar a Najeriya a Abuja.

An samu rabuwar kai tsakanin bagarorin masu zanga-zanga kan sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar a Najeriya a Abuja.

Masu zanga-zangar sun raba biyu ne,  inda sashi daya ke bore ga matsayar takwaransa,  kan sahihancin sakamakon zaben.

Rukunin farko na masu zanga-zangar sun bayyana rashin jin dadinsu da kin yin amfani da tsarin tattara sakamako na intane tda hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta  ce za ta yi da fari, tare da yin kira ga gwamnati da ta soke zaben.

Guda daga cikinsu mai suna Ilemona Onoja, ta ce babbar bukatarsu ita ce shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya cika alkawarin da ya dauka na yin zabe a bude.

“Dalili kuwa shi ne abin da ya yi wa ’yan Najeriya alkawari daban, amma kawai sai muka ga wani abun daban”, in ji ta.

Ita ma wata mai suna Lilian Kozau ta ce bai kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bari INEC ta bata masa suna ba a idon duniya, don haka ya soke zaben.

A hannu guda masu zanga-zangar adawa da wannan matsaya sun ce su kam.sun gamsu da sakamakon zaben ranar Asabar din, don haka INEC ta yi watsi da bukatar masu zanga-zangar farko.

Lawrence Beatrice, guda ce daga masu wannan ra’ayi, ta kuma ce kada INEC ta saurari masu adawa da sakamakon, domin ba su da hujjojin kare maganganunsu.

“Duk shaidun da aka tattara lokacin zabe sun nuna ingantacce ne, illa kalubalen da ba za a rasa ba.

“Muna yaba wa INEC da kuma fatan za ta ci gaba da gudanar da aikinta yadda ya kamata a zabe na gaba”.