✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin sakandare na ci mana tuwo a kwarya — Dagacin Kujama

Dakacin yankin Kujama da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna, Mista Stephen Ibrahim, ya koka kan yadda rashin makarantar sakandare a yankinsu ke ci…

Dakacin yankin Kujama da ke Karamar Hukumar Chikun a Jihar Kaduna, Mista Stephen Ibrahim, ya koka kan yadda rashin makarantar sakandare a yankinsu ke ci musu tuwo a kwarya.

Basaraken ya ce, sakamakon rashin makarantar a yankinsu ’ya’yansu da dama, musamman ma mata, sun kasa ci gaba da karatunsu bayan kammala firamare.

Ya ce kauyuka kimanin 15 ne yankin ke kunshe da su wanda ya kamata a ce gwamnati ta duba ta bude musu makarantar sakandare don amfanin ’ya’yansu.

Ibrahim ya yi wadannan bayanan ne a wajen wani taron masu fada a ji na yankin kan batun muhimmancin karatun ’ya’ya mata wanda suka gudanar a ranar Laraba.

A cewarsa, rashin makarantar sakanadare a yankin nasu ya yi sanadiyar yaran yankin da dama sun daina zuwa makaranta, musaman ‘ya’ya mata.

Yana mai cewa, yaran nasu kan yi tafiya mai nisan kilomita 15 kafin su je makaranta mafi kusa da su.

Ya ce kauyukan da lamarin ya shafa su ne; Danbushiya da Keke A da Keke B da Doka Mai Jamal da Sabon Gero da Kakura da Dan Hono da kuma Kaluga.

Sai kuma Kurmin Data da Kan Rafi da Sabon da Garin Kan Rafi da Torkachi da Kafari da Ungwan Sori da Buyaya da Karatudu da rukunin Gwamnati Tarayya da ke Gonin Gora.

(NAN)