✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin sabbin kudi ya yi ajajlin mai ciki a asibiti

Mijin matar ya ce an ki karbar ta a asibiti ne saboda ya kasa samun tsabar kudi daga banki da kuma POS da zai biya…

Wata matar aure ta rasu sakamakon takaddama kan rashin sabbin takardun kudin biyan kudin asibitinta a Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Takaddamar ta faro ne a yayin da matar take tsaka da nakuda a garin Kasuwar Magani, amma aka ki karbar ta a asibiti saboda mijinta ya kasa samun tsabar kudin da zai biya kudin da asibitin ya bukata.

Mijin matar, Mista James Auta, ya ce an ki karbar mai dakin tasa a asibiti ne saboda ya kasa samun tsabar kudi daga bankinsa da kuma POS da zai biya asibiti.

Aminiya ta gano cewa matar ta rasu ne bayan da ta haihu, amma jinin da ke zubowa ya ki tsayawa.

Lamarin dai ya jefa mutane cikin jimami, a yayin da ake fadi-tashin samun tsabar kudi domin biyan kudin asibiti da sauran bukatun yau da kullum.

A kwanakin baya dai Aminiya ta ruwaito Gwamnatin Jihar Kaduna na umartar asibitocinta su koma karbar kudi ta POS.

Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna (KDIRS) ta ce tun kafin sauyin kudi da kuma sabuwar dokar takaita amfani da tsabar kudi gwamnatin jihar ta yi dokar komawa biyan kudin asibiti ta hanyoyin zamani.

Matsalar karancin kudi

Batun sauyin kudi dai ya sanya ’yan Najeriya cikin damuwa, inda a halin yanzu tsabar kudi ke kamshin turaren dan goma.

’Yan kasar da dama sun nuna damuwarsu kan mawuyacin halin da daina amfani da tsoffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200 da aka sauya ya jefa su a ciki.

Gabanin cikar wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu na haramta amfani da tsoffin kudin ne Kotun Koli ta kara lokacin zuwa ranar Laraba 15 ga watan da muke ciki.

A ranar ce Kotun Kolin za ta fara sauraron karar da gwamnatocin wasu jihohin Arewacin Najeriya suka shigar suna neman karin wa’adin haramta amfani da tsoffin kudin.

A halin da ake ciki, tsoffin takardun kudin ma neman su ake yi ido rufe a bankuna da ATM da kuma wurin masu hadahadar kudi ta POS.

Wannan yanayi ya bai wa masu harkar POS damar cin karensu babu babbaka, inda a wasu wurare suke karbar cajin har kashi 20 cikin 100 a kan kudin da za a karba a hannunsu.

Babban Bankin Najeriya (CBN) dai na zargin zargin bankunan kasuwan ci da boye sabbin kudaden domin samun kazamar rabia, zargin da bankunan suka musanta.

Amma a makon jiya, Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) sun kai samame a rassan wasu bankuna, inda suka kama sabbin kudaden da aka boye.

A ranar Juma’a, Majalisar Koli ta Kasa ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya bugo karin sabbin takardun kudaden, ko kuma ya bari a ci gaba da amfani da tsoffin har zuwa lokacin da zai wadatar da ’yan Najeriya da sabbin takardun N200 da N500 da kuma N1,000.

Duk da haka kuma, a wasu wuraren ana kin karbar tsoffin takardun kudin.