✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin lafiyar Buhari ta kawo wa gwamnatinsa cikas —Adesina

Buhari zai bar Najeriya cikin nagarta fiye da yadda ya same ta a 2015.

Mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce rashin lafiyar da Shugaban Kasa ya yi a 2017 ta janyo wa gwamnatinsa nakasun aiki na watanni takwas a mulkinsa.

Adesina ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake zanta wa a gidan talabijin na Channels.

Adesina, wanda ya bayyana nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a yayin zantawar, ya ce shugaban ya shafe watanni takwas yana jinya a Ingila a 2017.

“Lokacin da ya soma rashin lafiya a watan Janairun 2017, ya dawo a watan Maris, ya sake komawa a watan Afrilu kuma bai dawo ba sai 19 ga watan Agusta.

“Wannan jinya ta dauki wata takwas ba tare da yana aiwatar da komai ba. Tabbas, babu wanda zai so hakan amma abun farin ciki shi ne daga baya ya samu lafiya.”

Sai dai ya ce duk da wannan koma baya da aka samu, shugaba Buhari zai bar kasar nan cikin nagarta fiye da yadda ya same ta.

Adesina ya bayyana cewa a shekarar 2015 lokacin da Buhari ya karbi mulki, kananan hukumomi 17 na hannun ‘yan ta’adda, amma daga bisani gwamnatinsa ta kwato su bayan karbar mulkin.

Game da tattalin arziki kuwa, ya yi nuni da cewa a yanzu Najeriya na da karfin tattalin arziki iri daban-daban a sakamakon kokarin da gwamnatin Buhari ta yi.

Hadimin ya ce duk da kalubalen da gwamnatin Buhari ta fuskanta baya ga rashin lafiyar da ya shafe wata takwas yana yi, ya yi manyan ayyuka na a zo a ga ni.

Idan ba a manta ba, a baya-bayan nan masu sharhi kan al’amuran siyasa na ganin cewar Buhari ya gaza cika alkawarin da ya yi na cire miliyoyin ’yan Najeriya daga kangin talauci.