✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Talata za a bude layukan sadarwa a Zamfara – Gwamna Matawalle

Ya kuma ce kasuwannin mako-mako su ma za su ci gaba da hada-hada.

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce ranar Talata mai zuwa za a dawo da hanyoyin sadarwar da aka toshe a wasu yankunan Jihar a watannin baya.

A ranar hudu ga watan Satumban 2021 ne dai aka toshe hanyoyin sadarwa a wasu sassa na Jihar a kokarin da ake yi na yaki da ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran ’yan ta’addan da suka addabi Jihar.

Sai dai a watan da ya gabata, an dawo da hanyoyin sadarwar a Gusau, babban birnin Jihar.

Da yake jawabi ranar Asabar, jim kadan da kammala zaben shugabannin jam’iyyar APC a matakin Jihar, Gwamna Matawalle ya ce za a dawo da hanyoyin sadarwar tare da dage haramcin cin kasuwannin mako-mako a Jihar.

A cewarsa, “Daga bayanan da muka samu, an samu ci gaba matuka wajen yaki da ayyukan ’yan ta’adda a Jiharmu. Saboda haka, nan da ranar Litinin ko Talata, mutanen wadannan yankunan za su samu damar yin mu’amala da ’yan uwansu ta waya.

“Muna daukar matakan da suka dace don tabbatar da cewa mun hana wadannan ’yan ta’addan sakat. Saboda in muna shan wahala, su ma suna sha. Dukkan wani mawuyacin halin da mutanenmu suka shiga sakamakon wannan matakin ya kusa zama tarihi,” inji Gwamnan.