A ranar 8 ga watan Maris kungiyoyin mata a kasashen duniya da daidaikun al’umma masu rajin kare hakkokin mata suka yi bikin zagayowar wannan rana a kasashe sama da 100, na duniya. Bikin, wanda aka fara a ranar 28-02-1909, a birnin New York na Amurka da shekara ta zagayo ne aka mayar da shi zuwa ranar 8 ga Maris din kowace shekara. Kuma tun daga 1910, ake yinsa a ranar 8 ga Maris din kowace shekara. Duk da a kasar Amurka aka fara bikin, amma kasashe masu bin akidar tsarin Gurguzu da Kwaminisanci suka fi yin bikin har zuwa 1975 da Majalisar dinkin Duniya ta amince da yin sa a duk fadin duniya duk shekara.
A lokacin bikin akan yi tarurruka da laccoci wani lokaci har da yin tattaki da sauran wasu harkoki na baza yekuwar irin gwagwarmaya da kalubalen da mata suke ciki na kuntatawa da cin zarafi, kamar fyade da bautarwa da nuna wariya wajen biyan hakki, ko samun madafun iko a ofis ko a kasuwa da abin da ya shafi harkokin siyasa da na zamantakewa baki daya. A wajen baza irin wannan yekuwa akan fitar da matsaya kan yadda za a tunkari wadannan matsaloli zuwa shekaru na gaba. Rana ce da ake kuma tunawa da irin nasarorin da mata suka samu a duniya ba tare da la’akari da bambancin kasa ko launi ko harshe ko karfin tattalin arziki ko na siyasa, bare kuma al’ada ba, wato akan kalli rawar da mace ko mata suka taka a lokacin bikin.
Akan yi la’akari da irin taken bikin kowace shekara kan halin da mata suke ciki, a kan abin da ke damunsu walau na rashin samun ingantattu kuma wadatattun ayyukan kiwon lafiya da fatara da rashin samun madafun iko a cikin harkokin tafiyar da mulkin kasa musamman a lokacin siyasa. Taken taron bana dai shi ne ‘Yanzu ne Lokaci: Gwagwarmaya a Birni da Karkara da za su sauya rayuwar mata.’
Mai karatu a takaice wannan shi ne dan bayani a kan dalilan bikin Ranar Mata ta Duniya, wadda a nan kasar Matar Shugaban kasa ko Gwamnan Jiha sukan shugabanci bikin ranar a kowace shekara tare da kungiyoyin mata. A bana a Abuja Uwargidan Shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari ta yi amfani da ranar wajen kaddamar da wani kamfe mai taken ‘KU kYALE MANA ’YA’YANMU MATA.’ Kamfen din bai rasa nasaba da sace ’yan matan Sakandaren Kimiyya da Sana’a ta garin Dapchi su 110 da kungiyar Boko Haram bangaren Albarnawi ta yi a ranar 19 ga Fabrairun da ya gabata. Sacewar da ta zo bayan shekara 4 da sace ’yan matan Sakandaren Chibok a Jihar Borno da aka yi ranar 14-4-2014. Bayan kaddamar da kamfen din Uwargidan Shugaban ta yi kira ga masu sace ’yan mata a makarantun sakandare da masu aikata miyagun halaye irin su fyade da cin zarafin mata da su yi wa Allah su daina, kuma ta yi fata kokarin da mahukunta suke yi na kwato ’yan matan zai cinma nasara. Daga karshe ta yi fatan kafafen watsa labarai da matan gwamnonin jihohi za su dauki wannan yekuwa nata na “Ku kyale ’Ya’yanmu Mata” su yayata shi zuwa ga kowa da kowa.
Ita ma wata sabuwar kungiyar mata mai suna MATA DON MATA da ta kunshi matan da suka fito daga jam’iyyun APC da PDP da APGA da LP sauran jam’iyyun siyasar kasar nan, a taron da ta yi da manema labarai a Abuja daya daga cikin jiga-jigan kungiyar kuma tsohuwar Ministar Harkokin Mata Hajiya Inna Ciroma, kokawa ta yi a kan yadda jam’iyyun siyasar kasar nan ba sa bin tanade-tanaden kundayen tsarurrukan mulkinsu da suka tanadi bayar da kashi 35, cikin 100, na dukan mukaman siyasa, na zabe ko nadi, ga mata duk da irin yadda su ke amfani da matan wajen cimma bukatunsu na zabe. Hajiya Inna Ciroma ta ce muddin ana son dimokradiyyar kasar nan ta ci gaba to lallai sai ana damawa da mata. Sauran kungiyoyin mata irin su Lauyoyi Mata ta Afirka da makamantanta irin wadannan kiraye-kiraye suka yi ta yi a kan cin zarafin mata da cewa lallai lokaci ya yi da za a daina, kuma a rika kula da lafiyar mata da ba su cikakken ilimi kowane iri da tallafa musu a kan hanyoyin dogaro da kai.
Mai karatu ka iya cewa lallai kam mata a baya suke a batun madafun iko a kasar bisa ga la’akari da mata 6 kadai ne ake da su a Majalisar Zartarwa mai ministoci 36, yayin da ake da zababbun mata 22, a Majalisar Dokoki ta kasa. Bakwai a Majalisar Dattawa, mai wakilai 109 da 15, a Majalisar Wakilai, mai wakilai 360. In aka gangaro zuwa jihohi, mata ba su wuce bibbiyu da ake nadawa kwamishinoni, a majalisun dokoki na jihohi kuwa nan ma ba kasafai ake jin muryar mata ba. Sauran nade-nade na masu ba da shawara ko mataimaka na musamman ko shugabanni da daraktoci a hukumomin gwamnatoci, nan ma matan ba su da wani kason a-je-a-karar.
Tunda an zo zamanin da ake batun ’yancin fadin albrakacin baki da neman hakki, shi ya sa ake jin muryoyin wadansu matan suna ta kururuwa a kan ana tauye hakokin mata. Ko da wai ba musu wadansu maza da iyaye na tauye hakkokin iyalinsu, amma abin da na yi imani, shi ne wasu hanyoyin da matan suke bi don neman gyara ba su ne mafita ba. A nawa dan tunanin akwai bukatar dukanmu Musulmi da wadanda ba Musulmi ba mu gyara tsarin auratayyarmu gyara na hakika, bisa ga tanade-tanaden addinanmu. Mai karatu zai ce me ya sanya duk irin miyagun abubuwan da suke faruwa na tsallake su na koma kan maganar aure? Ba don komai na yi batun auratayya ba sai don cewa auratayya ta kowace irin al’umma ita ke tabbatar da kyakkyawa kuma ingantacciyar al’umma. Koda kasashen da suka ci gaba da a yau muke ta hankorin koyi da su ba su fada cikin mawuyacin halin zamantakewar da suke ciki ba, sai da suka yi watsi da tsarin auratayyarsu.
Ta hanyar auratayya ce maigida zai iya daukar nauyin iyalinsa da dukan wadanda suka rataya a wuyansa gwargwadon yadda Allah Ya ce. Haka sauran al’umma a kan danginsu da makusantansu da marayu da sauaran mabukata. Su kuma matan wannan zamani da mazan a rika yin hakuri da rayuwa baki daya, ta hanyar rage buri, domin buri marar kan gado ke jefa al’umma musamman mata cikin mawuyacin halin rayuwar da yau suke cewa ana kuntata musu ana cin zarafinsu.