✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Asabar ce 1 ga watan Dhul Qadah 1442 —Sarkin Musulmi

Asabar ce 1 ga watan Dhul Qadah 1442 bayan hijirah.

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Harkokin Addinin (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayyana ranar Asabar 12 ga Yunin 2021 a matsayin 1 ga watan Dhul Qadah shekara ta 1442 bayan hijirah.

Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da Shugaban Kwamitin Gudanarwar na Majalisar, Farfesa Sambo Junaidu ya fitar a ranar Juma’a.

  1. Ganduje ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyin fadan daba a Kano
  2. Najeriya za ta sayar wa da kasashe hudu wutar lantarki

“Kwamitin Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci tare da hadin gwiwar Kwamitin Ganin Wata ba su samu labarin ganin sabon wata ba a fadin kasar nan ba.

“An fara duban watan Dhul Qadah na shekarar 1442 bayan hijirah a ranar Alhamis 10 ga Yuni, wanda yayi daidai da 29 ga Shawwal 1442 bayan hijirah.

“Sai dai saboda rashin ganinsa, ranar Juma’a 11 ga Yuni za ta kasance 30 ga watan Shawwal 1442 bayan hijirah.

“Sultan ya amince tare da bayyana ranar Asabar 12 ga Yuni a matsayin 1 ga watan Dhul Qadah 1442 bayan hijirah,” a cewar sanarwar.

Dhul Qadah ya kasance wata na 11 a cikin jerin watannin musulunci, kuma daya daga cikin watanni masu alfarma.

Kasancewarsa wata mai alfarma, an haramta yin yaki a cikinsa.

Watan da zai biyo bayansa shi ne watan Dhul Hijja, wanda a cikinsa ne al’ummar musulmi duniya wadanda suka samu iko ke gudanar da aikin hajji duk shekara.