✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rahma Sadau ta gana da daliban Najeriya a Indiya

Daliban Najeriya da ke karatu a Indiya sun gayyaci jaruma Rahma Sadau.

Jarumar Kannywood, Rahma Sadau ta gana da daliban Najeriya da suke karatu a Jami’ar Integral da ke kasar Indiya.

Jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram, inda ta ce, “Ina matukar farin ciki da alfaharin samun gayyata daga daliban Najeriya da ke karatu a Jami’ar Integral ta kasar Indiya.

“Na kasa boye farin cikina da wannan girmamawa da karamci. Ina godiya.”

Jaruma Rahma Sadau tare da jami’an Jami’ar Integral a lokacin ziyarar da ta kai. (Hoto: @rahamasadau)

Rahma Sadau ta kara godiya ga ma’aikatan jami’ar da sauran daliban makarantar bisa karamci da suka nuna mata.

Jami’an Jami’ar Integral a lokacin ziyarar da Rahma Sadau ta kai a ranar 14 ga watan Satumba, 2021. (Hoto: @rahamasadau)