✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PSG na son raba gari da Sergio Ramos

PSG ta shaida wa Ramos kudirinta na rabuwa da shi a karshen kakar wasanni.

Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain na son raba gari da Sergio Ramos a karshen kakar wasannin bana.

Kwantaragin Ramos zai kare a 2023, sai dai PSG na son warware yarjejeniyar da tsakaninta da dan wasan bayan nata a bana.

Rahotannin sun nuna masu ruwa da tsaki a PSG sun shaida wa dan wasan mai shekara 36 cewa ba ya daga cikin jerin ’yan wasan da kungiyar za ta yi amfani da su a kakar wasanni mai zuwa sakamakon rauni da yake yawan fama da shi.

Ramos ba ya son barin PSG

Har wa yau, duk da cewa kungiyar ta bayyana wa Ramos kudirinta a kansa, dan wasan ba ya son barin ta, yana son yin gogayya don kwatar gurbi a kungiyar.

Kungiyar ta fusata kan irin raunin da Ramos ke fama da shi a bana, wanda hakan bai ba shi damar buga ko wasa daya a Gasar Zakarun Turai ba.

PSG ta dauko Ramos ne daga Real Madrid don ya jagoranci ’yan wasan wajen lashe Zakarun Turai, amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, inda Real Madrid ta yi waje da ita a gasar.

Duk da cewa PSG na son rabuwa da dan wasan, amma za ta iya fuskantar tarnaki, saboda zuwa yanzu babu wata kungiya da ta nuna sha’awar daukar tsohon kyaftin din na Real Madrid.