✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pogba zai bar United, Hazard zai koma Chelsea, Kroos zai tafi Newcastle

Newcastle na sha’awar dan wasan tsakiya na Real Madrid da Jamus Toni Kroos.

An dakatar da tattaunawa tsakanin Paul Pogba da Manchester United kan batun tsawaita zamansa a kungiyar bayan shan kashi da United ta yi a hannun Liverpool in ji wakilansa Mino Raiola. (AS)

Mai tsaron baya Chelsea Antonio Rudiger zai iya barin kingiyar a karshen kakar badi, wanda ake alakanta shi da cewar zai koma taka leda a ko dai Juventus ko Manchester City ko Tottenham ko kuma Paris St-Germain. (Wettfreunde)

Barcelona na son karbar aron dan wasan tsakiya na Manchester United, dan Holland Donny van de Beek, mai shekara 24. (Sport )

Tottenham ta shiga tattaunawar da za ta kai ta ga daukar Antonio Conte domin ya maye gurbin Nuno Espirito Santo a matsayin mai horas da ’yan wasanta. (Tuttomercato)

Haka kuma, mai horas da ’yan wasan Porto Sergio Conceicao, mai shekara 46, yana daga cikin wadanda Tottenham ke duba yiwuwar dauka domin maye gurbin Nuno. (Standard)

A halin da ake ciki kungiyar ta Premier za ta nada Ryan Mason, mai shekara 30, a matsayin mai horas da ’yan wasan na wucin-gadi har zuwa lokacin Kirsimeti. (Football Insider)

Real Madrid ta zuba idonta don ganin yadda za ta kaya a kokarin da take na ganin ta janye dan wasan tsakiya na Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 28, da kuma dan bayan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 28. (Marca)

Haka kuma Paris St-Germain ta Faransa na sauraren yadda lamarin Pogban zai kasance a Manchester United. (Le10 Sport)

Shi kuwa dan bayan Faransa Theo Hernandez, mai shekara 24, zai yi watsi ne da shirin Manchester City na zawarcinsa, inda zai kulla sabuwar yarjejeniyar ci gaba da zama a AC Milan. (Calciomercato)

Manchester United ta rasa damar daukar dan wasan tsakiya na PSG da Senegal Idrissa Gueye, mai shekara 32, a bazarar da ta wuce saboda ta kasa gabatar da wani kwakkwaran tayi inda ‘yn wasa da dama suka tsaya a kungiyar. (Mail)

Har yanzu Arsenal na sa rai a kan dan wasan tsakiya na Real Madrid da Sifaniya Dani Ceballos, mai shekara 25, duk da yadda ba ta saye shi ba bayan zaman aro na shekara biyu a kungiyar. (El Nacional)

Newcastle na sha’awar dan wasan tsakiya na Real Madrid da Jamus Toni Kroos mai shekara 31. (El Nacional)

Kungiyar ta Pemier ba ta damu da yawan albashin da Aaron Ramsey yake bukata ba a shirin da take na sayo dan wasan na tsakiya dan Wales, mai shekara 30 daga Juventus a watan Janairu. ( Mirror)

Haka kuma kungiyar ta Newcastle ta na son kociyan Ajax Erik ten Hag ya zama sabon mai horad da ‘yan wasanta amma kuma tana fuskantar kalubalen yadda za ta shawo kansa ya yarda. (Mirror)

Everton da kuma West Ham suna cikin masu rubibin dan kwallon Inter Milan, Ivan Perisic ciki har da kungiyoyin da ke buga Bundesliga. (Fichajes)

Newcastle United sai ta tanadi kudi mai tsoka idan har tana son daukar kocin Ajax, Erik ten Hag domin maye gurbin Steve Bruce wanda ta kora. (Chronicle Live)

Dan kasar Brazil, Marcelo ya sanar da Real Madrid cewar yana son barin kungiyar a karshen kakar bana. Watakila kungiyar Brazil wato Fluminese zai koma da taka leda. (El Nacional)

Mai horas da ’yan wasan kungiyar West Ham, David Moyes ya ja kunnen duk kungiyar da ke son daukar Declan Rice ta tanadi fam miliyan 100. (Manchester Evening News)

Chelsea ta fara duba yiyuwar dan kwallon Porto, Luis Diaz wanda Newcastle da Bayern Munich da kuma Real Madrid ke zawarci. (Nicolo Schira)

Chelsea da Newcastle United na daga cikin kungiyoyin da ke buga gasar Premier wadanda aka ankarar da su kan yiwuwar su iya sayen dan wasan gaban Belgium Eden Hazard mai shekara 30 daga Real Madrid a watan Janairu. (ESPN)

Tuni dai mai horas da kungiyar, Carlo Ancelotti, ya sanar cewa dan wasan na iya kama gabansa, inda a makon da ya gabata ya tabbatar da cewa dan wasan lafiyarsa kalau sai dai ba shi da ra’ayin sanya shi a wasanni (Goal)

Kwarin gwiwar da Newcastle ke da shi na sayen dan wasan gaban Barcelona da Faransa mai shekara 24 Ousmane Dembele ya ƙaru sakamakon Barcelona sai ta biya tsohon kocinta Ronald Koeman diyyar fam miliyan 10 bayan sallamarsa da aka yi. (Express)

Ita ma Manchester United sai ta biya Ole Gunnar Solskjaer diyyar fam miliyan 7.5 muddin kulob din ya yanke shawarar sallamarsa a halin yanzu. (Sun)

United ta soma cire rai daga daukar tsohon kocin Inter Milan Antonio Conte domin maye gurbin Solskjaer sakamakon irin kudin da kulob din zai biya. (Star)

Sai dai Antonio Conte din ba ya son karbar aikin horas da kungiya a tsakiyar kaka. Ana danganta tsohon kociyan na Chelsea da Inter Milan da aiki a Manchester United ko Newcastle United. (Todofichajes)

Bayanai sun ce West Ham na tattaunawa da hamshakin mai kudin kasar Czech din nan Daniel Kretinsky kan yiwuwar ya sayi kashi 27 cikin 100 na kulob din, inda ake ganin nan gaba ma zai saye kulob din baki daya. (Sky Sports)

Ashe sai da Manchester United ta tunkari Inter Milan domin sayen dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku a bara gabanin komawar dan wasan Chelsea a watan Agusta in ji wakilin dan wasan. (Telegraph)

Arsenal za ta fafata da Barcelona a yunkurinta na sayen dan wasan gaban Manchester City Raheem Sterling. (Footbal.London)

Gunners din na kuma sa ido kan halin da dan wasan Borussia Monchengladbach mai shekara 24 yake ciki wato Denis Zakaria wanda akwai yiwuwar dan wasan ya tafi a kyauta a kaka mai zuwa. (Sun)

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya roki shugabannin Chelsea da su sayi wani dan wasan gaba a watan Janairu domin rage nauyin da ke kan Lukaku. (Transfer Window Podcast via Express)

Dan wasan tsakiyan Southampton da Ingila James Ward-Prowse na daga cikin wadanda Newcastle ke nema a watan Janairu duk da cewa dan wasan mai shekara 26 zai saka hannu a sabuwar yarjejeniya da kulob dinsa a kaka mai zuwa. (Football Insider)

Dan wasan Manchester United din nan na kasar Netherlands mai shekara 24 Donny van de Beek da kuma dan wasan bayan Ivory Coast mai shekara 27 Eric Bailly na ci gaba da neman a basu tabbaci kan makomarsu a kulob-kulob dinsu. (Sun)

Chelsea na da tabbacin dan wasan bayan Denmark Andreas Christensen mai shekara 25 zai saka hannu kan kwantiragi mai tsawo a Stamford Bridge. (Football Insider)

Juventus ta shiga rububin sayen dan wasan gaban Jamus da Red Bull Salzburg mai shekara 19 Karim Adeyemi. (Calciomercato)

Tottenham ta shirya barin dan wasan tsakiyar Ingila Dele Alli mai shekara 25 ya bar kulob din a watan Janairu. (Athletic)

Liverpool na duba yiwuwar sayen dan wasan gaba na Real Madrid da Serbia Luka Jovic, mai shekara 23. (Fichajes)

Liverpool za ta bar mai tsaron ragarta dan Jamus Loris Karius, mai shekara 28, ya tafi a kyauta a watan Janairu- rabonsa da tsare ma ta raga tun 2018. (Mirror)

Tottenham na fuskantar gogayya daga Bayern Munich kan zawarcin dan wasan gaba na Nantes Randal Kolo Muani wanda take son dauka a karshen kakar nan. Dan gaban dan Faransa mai shekara 22, zai kasance ba shi da kungiya a lokacin bazara. (Foot Mercato)

Abokan Donny van de Beek a Manchester United suna ba dan Holland din mai shekara 24, shawara a kan ya sauya wakili domin ya samu damar barin Old Trafford. United ta tattauna da Everton da Wolves kan daukarsa aro. (Mail)

Liverpool na matukar sha’awar sayen dan wasan gaba na gefe na Leicester da Ingila Harvey Barnes, mai shekara 23. (Fichajes)

Tottenham ta bi sahun Leeds a kokarin sayen dan wasan gaba na Espanyol kuma dan Sifaniya Raul de Tomas, mai shekara 27. (Sport Witness)

Crystal Palace za ta katse aron da ta karba na dan wasan gaba na Jean-Philippe Mateta a watan Janairu. Dan Faransan mai shekara 24 yana zaman aro ne daga Mainz har zuwa karshen kakar nan, to amma kuma ba ya cikin tsarin kociyan kungiyar, Patrick Vieira. (Sun)

Derby na son sayar da mai tsaron ragar Scotland David Marshall, mai shekara 36, a watan Janairu. (Sun)