✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta nada Akinwonmi a matsayin Shubaban Rikon kwarya

PDP ta nada Akinwonmi a matsayin shugaban rikon kwarya na jam'iyyar.

Kokarin Uche Secondus na ci gaba da rike mukaminsa a yayin da rikici ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya kare a ranar Alhamis, bayan da jam’iyyar ta nada Yemi Akinwonmi a matsayin Mukaddashin Shugaban Jam’iyya na Kasa.

Bayan da wata Babbar Kotun Jihar Ribas ta dakatar da Secondus a ranar Litinin, mataimakansa, Akinwonmi daga yankin Kudu da Suleiman Nazif daga yankin Arewa, kowannensu ya  ayyana kansu a matsayin wanda ya maye gurbin Secondus.

Sai dai daga bisani an cim-ma yarjejeniya a kan Akinwonmi ya zama Shugaban Rikon Kwarya har zuwa lokacin da Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar zai kara zama.

A karshen taron, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Olagbondiyan, ya sanar da cewa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun tsayar da Akinwonmi a matsayin Mukaddashin Shugaba.

“A bayyane zan iya cewa a madadin jam’iyyarmu, mun bi diddigin rikicin, kuma a yau, kamar yadda duk kuka shaida, mun zo ne don tabbatar da cewa an gabatar da karar kuma gaba daya an amince da Dattijo Yemi Akinwonmi a matsayin Mukaddashin Shugaban babbar jam’iyyarmu.

“Yana da kyau ku da sauran ’yan Najeriya ku sani cewa wannan ya yi daidai da tanadin tsarin mulkin jam’iyyar.

“Za mu sake yin wani taron na kwamitin a gobe kan shirye-shiryen gudanar da taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, wanda zai gudana ranar Asabar.”

Secondus ya fuskanci matsin lamba inda aka rika kira ya sauka daga mukaminsa har sai da kotu ta dakatar da shi daga ci gaba da shugabancin PDP.