✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PCNI da bSF sun horar da sababbin kafofin labarai a Yola

A ranar Litinin da ta gabata ce Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) da kuma Gidauniyar Tallafawa Wadanda Rikici ya Shafa…

A ranar Litinin da ta gabata ce Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) da kuma Gidauniyar Tallafawa Wadanda Rikici ya Shafa (bSF) suka shirya taron bitar na wuni uku don horarwa kan “Amfani da Sababbin Kafofin Watsa don Bayar da Rahotannin Ayyukan Jinkai da Ci gaban Jama’a” a Yola Jihar Adamawa. 

Shugaban Sashen Yada Labarai da Sadarwa na Kwamitin PCNI, Alkasim Abdulkadir ya ce an shirya wannan taron bitar ne don nuna karfin sababbin kafofin watsa labarai wajen yayata labaran da suka shafi Arewa maso Gabas – yankin da ake kallon ya yi nesa da kafafen watsa labarai.

Ya ce, fadada kwarewar masu watsa labarai a yankin zai yi matukar inganta bayar da rahotannin dimbin ayyukan da gwamnati take yi wajen sake ginawa da gyara yankin.

A jawabin Babban Daraktan Gidauniyar bSF, Farfesa Sunday Ochoche ya bukaci mahalarta taron su ilimantar da junansu wajen amfani da wadannan kafofi don maida labaran nasu daga kanana zuwa manya da duniya za ta kalla. 

Sai ya yi marhabin da yunkurin karfafa aikin manema labarai a yankin inda ya bukace su kan su yi amfani da karfafan kafofinsu wajen yada akidar sanin mutuncin kai da kula da amana.

Ko’odinetan PCNI na Jihar, Barista Bello Diram, wanda ya halarci taron, ya yaba wa kokarin PCNI da bSF bisa shirya bitar sannan ya bukaci mahalarta taron su yi amfani da kwarewar da suka samu domin kyautata ayyukan jinkai.