✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Oshiomhole ya gana da Buhari a fadar shugaban kasa

Shugaban Jam’iyyar APC da kotu ta dakatar, Adams Oshiomhole, a yanzu haka yana ganawar sirri shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Aso…

Shugaban Jam’iyyar APC da kotu ta dakatar, Adams Oshiomhole, a yanzu haka yana ganawar sirri shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa a Abuja.

Ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da dalilin ganawar da Oshiomhole ke yi da shugaban ba.

A ranar Laraba ne wata babbar kotu a Abuja ta dakatar da Oshiomhole, a matsayin Shugaban APC na kasa.

Mai shari’a Danlami Sench, na kotun ne ya bukaci Oshiomhole, ya sauka daga mukaminsa sakamakon wasu kararraki da aka shiga na shirin tsige shi daga mukaminsa.