✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Oshiomhole: Gwamnonin APC 16 sun gana da Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC 16, rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da ganawar ne don sanin matsayin shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole…

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC 16, rahotanni sun bayyana cewa, an gudanar da ganawar ne don sanin matsayin shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole da aka dakatar.

Gwamnonin da suka halarci ganawar da shugaba Buhari sun hada da: Borno, Legas, Ogun, Edo, Kebbi, Jigawa, Kwara, Nasarawa, Neja, Filato, Ondo, Kano, Osun, Katsina, da Imo, da jihar Gombe.

A cikin Gwamnonin APC 20, hudu ne kadai ba su halarci ganawar ba, wadanda suka hada da: Kaduna, Yobe, Kogi, da Ekiti.