✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Orji Uzor Kalu: Za mu koma kotu nan take –EFCC

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Najeriya (EFCC) ta ce a shirye take ta sake fuskantar tsohon gwamnan jihar Abia,…

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Najeriya (EFCC) ta ce a shirye take ta sake fuskantar tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, a kotu kuma nan take.

Hukumar ta fadi haka ne a wata sanarwa da ta fitar tana mayar da martini ga hukuncin Kotun Koli ta Najeriya wadda ta yi fatali da hukuncin da aka yanke wa dan majalisar dattawan da wani tsohon jami’in gwamnatinsa, da kuma kamfaninsa.

Hukumar ta EFFC ta ce hukuncin Kotun Kolin abin takaici ne, amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba, saboda hujjojin da take da su a kan Mista Kalu ba za su kankaru ba.

“Har yanzu tuhume-tuhumen da aka yi wa Kalu suna nan, saboda Kotun Kolin ba ta wanke shi ba.

“Za a bude daukacin taskar dabarun gabatar da kara na EFCC a wata sabuwar shari’a, inda komai daren dadewa za a yi adalci”, inji EFCC.

Ranar Juma’a ne dai Kotun Kolin ta soke hukuncin tana cewa alkalin da ya yanke shi ba shi da hurumin yin haka saboda an yi masa karin girma zuwa Kotun Daukaka Kara a lokacin.

Ta kuma ce amfani da sashe na 396(7) na Dokar Hukunta Manyan Laifuffuka ta 2015 da aka dogara da shi aka bai wa Mai Shari’a Mohammed Idris damar zuwa ya kammala shari’ar ya saba wa Kundin Tsarin mulkin Najeriya.

Don haka ne Kotun Kolin ta ba da umarnin a sake shari’ar.

Ranar 5 ga watan Disamban bara ne dai aka yanke wa Orji Uzor Kalu, wanda dan majalisar dattawa ne, hukuncin zaman kaso na shekara 12; kuma yanzu haka yana garkame a gidan yari na Ikoyi.