Wai da gaske akwai cutar mantuwa, idan akwai yaya ciwon ya ke kuma me yake kawo shi, ko akwai hanyoyin da za a bi don magance shi ko kiyaye aukuwarsa?
Amsa: Bacewar tunanin abin da ya faru a baya shi muka fi kira mantuwa a kimiyyance. Ma’anar mantuwa tana hadawa da rashin rike bayanai a ka. Wato da wanda ya fiye manta abubuwan da suka shude da wanda ba ya rike abubuwan da za su faru ko kuma abubuwan da za a koya masa a gaba, duk sunansu masu mantuwa. Haka ya kamata a gane kwakwalwar masu karancin shekaru ta fi ta manya rike abu; wato bayani a kan yaro kamar rubutu ne a kan dutse, sabanin bayani a kan wanda kwakwalwarsa ta tsufa, wanda yake tamkar rubutu ne a kan ruwa. Abin da ya riga ya zo a addinance, to haka yake ma a kimiyyance. Don haka duk wanda ya fara tsufa dole ne zai iya samun yawan mantuwa, a wasu lokutan ma ya zama ciwon mantuwa (dementia). Wato akwai bambanci a tsakanin yawan mantuwa ke nan da ciwon mantuwa.
Me ke kawo ciwon?
Akwai wasu bangarori a tsakiyar kwakwalwa, wadanda suke da alhakin rike bayanai domin a tuna idan lokacin bukatar hakan ta taso. A mafi yawan lokuta ban da tsufa akwai cututtuka da dama da kan taba lafiyar wadannan bangarori na kwakwalwa, su jawo mantuwa. Ga misalan cututtukan:
1-Buguwa ta hadari: Misali buguwar hadarin mota ko na faduwa da sauransu. Wannan yakan jawo gushewar tunani na wani dan lokaci a mafi yawan lokuta. Amma idan buguwar mai karfi ce sosai, akan iya samun bacewar dukan abubuwan da suka faru a baya.
2-Tsufa ko girma: Tsufa yakan sa duka bangarorin kwakwalwa, (har wanda ke kula da tuna baya) su motse. Shi ya sa za a ga yawancin tsofaffi suke da mantuwa sosai.
3-Mutuwar barin jiki (stroke).
4-Yawan shan barasa yakan iya sa ciwon mantuwa.
5-Sai rashin wasu sinadaran bitamin da kwakwalwa kan bukata wajen aiki. Wadannan sinadarai sun hada da bitaman na rukunin B.
6-Akwai kuma wadanda aka samu cewa wasu magunguna sukan sa su kasa tuna baya. Wadannan magunguna sun hada da irin kayan maye da wadansu kan sha kamar baliyan ko kuma allurar barci da akan yi wa mutum a asibiti kafin a yi tiyata.
Mene ne alamu?
Ga mai yawan mantuwa, tunani yakan iya bace wa mutum haka kurum, na wani dan lokaci ko kuma na har abada. Bacewar tunani na wani lokaci wanda Hausawa kan kira sha’afa ba ciwo ba ne, wani hali ne na kowane dan Adam. Kusan kowa yakan yi fama da irin wannan mantuwa ta dan wani lokaci. Idan mantuwa ta yi yawan da takan rikita al’amuran mutum na yau da kullum ne, ko kuma ta zama ta har abada, to ta zama ciwo.
Shi kuma ciwon mantuwa alamominsa sun hada da yawan tambayoyi a kan lokacin da ake, da a wasu lokutan ma rashin sanin inda mutum yake, da neman sanin abin da gari ke ciki a ranar. Akwai kuma yawan maimaita abubuwa kamar aikace-aikacen gida, Sallah da sauransu.
Wasu lokuta hankali ma kan dan gushe. Amma ya kamata a gane cewa akwai bambanci a tsakanin gushewar hankali da ciwon mantuwa. Wato a mafi yawan lokuta, mai ciwon mantuwa a iya cewa kalau yake idan ba a zauna da shi na tsawon kamar yini guda ba, sabanin wanda yake da gushewar hankali.
Hanyoyin kariya daga matsalar ke nan su ne hanyoyin kiyaye wadannan abubuwa da aka zayyana a sama. Misali:
1-Kiyaye buguwa daga abin hawa ta hanyar sa hular kwano idan an hau budadden abin hawa kamar babur.
2-Daina shan giya da taba sigari (yawan shan sigari kan iya kawo ciwon mutuwar barin jiki).
3-Daina shan ababen maye.
4-Yawan amfani da ganyayyakin lambu da na ’ya’yan itatuwa saboda kwakwalwa ta samu sinadaran bitaman da take bukata.
5-Ga dalibai kuma yawan bita an tabbatar yana rage yawan manta karatu, don haka sai ana yawan bibiyar abin da aka koya a baya.
6-Tsofaffin ma yawan karance-karance da wasannin wasa kwakwalwa yana kaifafa basira domin kiyaye wannan matsala.
Bincike ya tabbatar da cewa mutanen da suka tsufa suna tare da ’yan uwa a kowane lokaci ba su cika samun wannan matsala ba.
Ga masu yawan mantuwa ko irin wadannan cututtuka masu kawo mantuwa, ba wani magani da za a iya ba su domin yawancin cututtukan kwakwalwa sukan yi wahalar warkewa. Sai dai akwai dabaru da akan yi a rage wa mutum wahalhalun da suke tattare da yawan mantuwa. Wadannan su ne yawan yin amfani da dan littafin shirya bayanai da jadawalin abubuwan da mutum ya saba yi, (diary).
A yanzu ma akwai irin wannan littafi na na’ura mai kamar wayar tafi-da-gidanka, kamar na’urar kwamfutar hannu da ake kira PDA ko palmtop. Yawanci masu wannan matsala wannan na’ura suke samu sai su zauna su zayyana ko a zayyana musu jadawalin aikace-aikace ko abubuwan da suka kamata mai ciwon ya yi a kowane lokaci da kuma harkokin da ya saba.
Wannan kimiyya takan taimaka wa masu wannan matsala yin rayuwarsu kusan ba tare da wata mushkila ba, tunda kusan duk tunaninsu an zuba shi a na’urar, sai dai kawai mutum ya danna na’ura ta tuna masa abin da ya kamace shi da yi.
Ina da ciwon daji, sai ya warke, sai ya dawo shi ne nake neman shawara.
Daga Sulaiman Giwa, Kaduna da Abdul A
Amsa: A’a ba dai ciwon daji ba. Ciwon daji ba ya irin haka. Kun san an ce karamin sani kukumi ne, idan kuna so a san ko wane irin ciwon ne sai kun je likita ya ga wurin.
Me ya sa wadansu mutane idan suka tashi daga barcin rana idanunsu ke yin ja, shin hakan matsala ce?
Daga Auwalu Akuyam
Amsa: Watakila barcin ne bai isa ba, shi ya sa maimakon su washe suka yi ja. Amma fa a wasu lokuta haka kawai zai iya faruwa ba wata matsala.
Shin cin dan itacen bado na da amfani ga jiki?
Daga Umar Haruna, Akuyam
Amsa: Bado wani dan itace ne da mukan ci a kasar Hausa a lokutan baya, a yanzu ba zan sani ba ko ana samunsa a kauye. Yana da ’ya’ya kamar kwan kifi haka masu bauri-bauri da yauki in ana tauna shi. Sinadaran amfani da ke cikinsa bincike ya nuna su ne na calcium da magnesium da niacin wadanda jiki ke bukata sosai.