✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NECO na bin jihohin Arewa bashin kudin jarabwa N2.8bn

Jihohi shida sun ki biyan N1.8bn na jarabawar da dalibansu suka zana a 2019.

Hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) ta ce tana bin gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya bashin Naira biliyan 2.8 na kudin jarabawar dalibansu.

Shugaban NECO, Farfesa Dantani Wushishi, ya ce taurin bashin da jihohin Arewan suke yi wake biyan kudin jarabawar daliban da suka dauki nayin na kawo wa ayyukan hukumar cikas.

“Gwamnatocin jihohin na alkawarin za su biya kudin jarabawar da dalibansu ke rubutawa, amma idan lokacin biya ya zo sai su ki, kuma hakan ya jefa hukumar cikin matsala.

“Muna bin jihohin Kano, Zamfara, Adamawa, Gombe, Borno da Neja bashin Naira miliyan 1.8 na jarabawar da dalibansu suka zana a 2019”, inji shugaban hukumar a lokacin da yake jawabi a garin Minnna, ranar Asabar.

Da yake cewa yawancin jihohin da hukumar take bi bashi ba sa biya, Farfesa Wushishi ya ce ya kamata gwamnatocin jihohin su kasance masu mutunta alkawari ko da hukumar ba ta rike sakamakon jarabawar daliban jihohinsu ba.

Ya bayyana cewa a halin yanzu hukumarsa na bin hanyoyin tattaunawa da gwamnatocin jihohin da take bi bashi domin ganin yadda za a samu mafita daga matsalar.

Wushishi ya ce ya kamata gwamnatocin masu taurin bashi su fahimci cewa da kudaden ne NECO take sayen kayan da take bukata domin gudanar da jarabawar dalibai masu kammala makarantar sakandare da kuma biyan jami’an da suka yi aikin jarabawar.

Don haka ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewan da su gaggauta biyan basukan su domin hukumar ta iya gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.