✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDDC: Majalisa ta kalubalanci Akpabio ya kai kara

Wadanda ake zargin sun karbi kwangilar NDDC sun ce ya kai a yi bincike

Majalisar Dattawa ta kalubalanci Ministan Neja Delta Godswill Akpabio ya kai sunayen ’ya’yanta da suka karbi kwagila a hukumar raya yankin (NDDC) ga hukumomin yaki da zamba domin cincike.

Shugaban Kwamitin Majalsiar kan NDDC Peter Nwaobushi wanda ke cikin Sanatocin da ake zargi, ya ce “idan har Akpabio na da hujjojin da ke tabbatar da zargin”, to ya kai bayanan ayyukan da yake zargi ga hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci da rashawa su yi bincike.

Binciken badakalar kwangilar ya yi sabon juyi ne bayan bullar wasikar Akpabio ga Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, yana ambatar sunayen ’yan majalisa da suka karbi kwangilolin NDDC da ke karkashin ma’aikatarsa.

‘Yan Majalisa da suka karbi kwangilar NDDC

Akpabio ya ce Nwaoboshi ya karbi ayyuka 53 sannan Sanata James Manager da Matthew Urhoghide suka samu shida-shida.

Sauran su ne Sanata Samuel Anyanwu, 19 sai wasu da ya kira ‘yan Majalisar Waikilai daga Ondo da Edo.

Babban Darektan Ayyuka hukumar Cairo Ojougboh, a cikin wani jabawabi ya tabbatar da matsayin Akpabio.

Ojougboh ya ce Sanata James James Manager da Sanata Peter Nwaoboshi da dan Majalisar Wakikai Nicholas Mutu, su ne kan gaba a wajen karbar ayyukan.

Neman kawar da hankali suke yi

Amman Sanata Nwaobushi da kuma Manager wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin Majalisar Dattawan sun musanta zargin.

Nwaobushi ya zargi Akpaio da yi wa kwamitin binciken badakalar biliyan 81.5 a NDDC yarfe domin kawar da hankalin jama’a daga almubazzarancin shugabannin rikon hukumar da dukiyar gwamnati, tare da yunkurin na boye barnar da sunan binciken kudade mara lokacin karewa”.

Kotu ce za ta raba mu

A nasa bangaren, Sanata Manager, ya yi barazanar maka Ojougboh a kotu kan zargin da ya ce ba shi da asali.

A cewarsa, tun da ya bar shugabancin kwamitin a 2015 ba kara zuwa ofishin NDDC ko wani reshenta ba ballantana shi ko wani kamfaninsa ya karbi kwangilar hukumar.

“NDDC ba ta taba bai wa wani kamfani mallakina kwangila ba, kuma ban taba sanin wani kamfani na ba da taba neman kwangilar gwamnati a fadin duniyar nan.

Ya kuma kalubalanci Ojougboh da ya gabatar da hujjar da ke tabbatar da zargin inda ya ce, “Wadannan masu neman bata mani suna sun san cewar akwai abin da zai biyu baya.

Daga cikin abubuwan da ya bukaci Ojougboh ya gabatar sun hada da sunayen ayyukan da aka ce ya yi, da kudin da aka biya shi, da inda aikin ya tsaya da sauransu.

Akpabio ya yi amai ya lashe

A baya, a wata wasika da Akpabio ya aike wa Gbajabiamila wanda ya ba shi wa’adin kwana biyu ya fallasa ’yan majalisar ko ta daure shi, ya musanta cewa ya zargi ’yan majalisa da karbar kashi 60% na kwangilolin NDDC.

Ya bayyana cewa shi ba ce haka ba, duk da cewa yana amsa tambayar da ’yar kwamitin majalisar da ke binciken ta yi masa ne.

NDDC ta fara jan hankalil ne sun lokacin da majalisar ta fara gano an kashe sama da Naira biliyan uku a hukumar da sunan tallafin cutar COVID-19 a cikin wata uku.

Asalin rikicin badakalar NDDC

Sabon rikicin ya samo asali ne bayan majalisar ta bankado badalar biliyan N81.5 a NDDC cikin wata biyar kacal.

Binciken wanda ya tayar da kura ya kara daukar hankalin jama’a ne bayan ’shugabannin hukumar sun zargi shugaban kwamitin Majalisar Wakilai wanda daga bisani ya saukda daga mukamin.

Hankali ya kara komawa kan lamarin ne bayan shugaban rikon NDDC Kemebradikuma Pondei ya yanke jiki a lokacin da kwamitin majalisar da ke binciken yake tsaka da yi wa ‘yan kwamitinsa tambayoyi.

A zama na gaba ne Akpabio a lokacin jawabinsa ga kwamitin ya zargi ’yan majalisar tarayya da karbar akasarin ayyukan NDDC.