Hukumar Sadarwa Ta kasa (NCC) ta ce tana kokarin hada gwiwa da masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa don wayar da kan masu hulda da layin sadarwa don su rika kiran layin neman taimakon gaggawa na 622 Toll-free 622 line). Wannan sabon layi ne da NCC ta bullo da shi inda al’umma za su rika kiran layin suna bayyana matsalolin da suka fuskanta don a magance musu cikin gaggawa.
Mista Abdullahi Maikano, Daraktan hulda da sashen al’umma na NCC ne ya bayyana haka a Legas a taron hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa da ake yi kowane wata uku da ake masa lakabi da (ICAF).
Taken taron shi ne: Gano matsalolin da al’umma ke fuskanta a bangaren sadarwa da kuma yunkurin magance su”.
Maikano ya ce bullo da layin 622, wata dama ce ga masu hulda da layukan waya su rika kiran lambar 622 a duk lokacin da suka fuskanci wata matsala daga kamfanonin wayoyin sadarwar da suke hulda da su.
Ya ce akwai bukatar kungiyoyin da ke kare hakkin masu amfani da layin sadarwa su rika fadakar da al’umma muhimmancin amfani da layin 622 da NCC ta bullo da shi, don su rika kiran layin don bayyana kokensu.
Ya ce, bangaren sadarwa yana da tsari mai kyau ganin kowane kamfanin sadarwa yana da layin da yake ba masu hulda da shi su rika kira don bayyana matsalolinsu.
“NCC tana kokarin wayar da kan al’umma game da bullo da layin 622, kuma kyauta ne kiran layin, ba a cire ko sisin kwabo.
“Yakamata kungiyoyin da ke kare hakkin masu amfani da layukan sadarwa suna da alhakin karbar kararraki daga masu amfani da layukan sadarwa don sanar da kamfanonin sadarwar, idan kuma suka ki daukar matakin da ya dace, to za su iya sanar da Hukumar NCC”.
Farfesa Felicia Monye, Shugabar kungiyar da ke fafutukar kwato wa masu hulda da kamfanonin sadarwa a Najeriya hakki, (ICAF) ta ce burin kungiyarsu shi ne su rika share hawayen masu amfani da layukan sadarwa a duk lokacin da suka fuskanci wata matsala.
Monye ta kara da cewa, yakamata kwastamomi su sani cewa a kowane lokaci su ne sarakuna amma kafin nan ya dace su rika sanin hakkokinsu da ya rataya a kan kamfanonin sadarwar da suke hulda da su, don kada su rika zaluntarsu.
“Ya kamata su rika sanin hakkinsu a shari’ance. Su rika sanin hakkinsu don hakan ne zai hana kamfanonin danne musu hakki”.
“A kan haka ne kungiyarmu za ta rika sanya ido a kan kamfanonin sadarwar don ganin ba su tauye wa kowa hakki ba”, inji ta.
Ta ce dalilin kafa kungiyar shi ne don ta rika fadakar da kwastamomi hakkinsu a kan kamfanonin sadarwar da suke hulda da su a Najeriya.
A nata jawabin Oluwaleke Ogundipe, Darakatar kula da bangaren kare hakkin masu hulda da kamfanonin sadarwa a Najeriya (CPC), ta ce an kafa kungiyarsu ce don kare hakkin kwastamomi sai dai akwai bukatar kwastomomin su rika sanin hakkinsu a kowane lokaci don kada a rika cutar da su.
Ta ce duk kwastoman da ya san hakkinsa to nan take zai rika nema don a share masa hawaye a duk lokacin da ya fuskanci wata matsala daga kamfanonin sadarwar da yake hulda da su, ba tare ma da sanin kungiyoyin kare hakkin ba.
Don haka ta nuna akwai bukatar a ci gaba da wayar da kan al’umma a game da sanin hakkokinsu da kuma hanyoyin da yakamata su bi don a magance su. (Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ne ya ruwaito.