Sakamakon karuwar almundahana ta amfani da harkar banki ta Intanet a Najeriya, Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) za hada hannu da Babban Bankin Najeriya (CBN) da saura masu ruwa-da-tsaki a fannin domi yaki da matsalar.
Hukumar NCC a wajen wani taron bitar ganawa na wuni daya a Fatakwal fadar Jihar Ribas, ta ce wajibi ne a hada hannu don yakar matsalar.
Bitar mai taken: ‘Masana’antu uku kan almundahanar Intanet a banki,” ta samu hakartar masu lacca da dama kan hanyoyin da za a iya bi a magance karuwar almundahanar da ake samu a bankuna.
Da yake gabatar da lacca, Adewale Banjoko, wani Babban Jami’in Tuntuba a Kamfanin kwararru kan Almundahana da Daddale masu Almundahana mai suna Global Fraud & Forensic Consultants Limited, ya bayyana cewa yana da kyau a fadada kamfe din wayar da kan jama’a kan almundahanar da ake tafkawa a bangaren bankuna har zuwa kan kananan yara da wadanda suke karatu a jami’o’in daban-daban.
Ya bayyana cewa kididdiga ta nuna cewa wadancan mutane da suke shekarun da aka ambata ne suka fi aukawa cikin waccan badakala idan ba a kula da su yadda ya kamata ba.
Ya kara da cewa, ’yan sanda da bangaren shari’a suna da dimbin aiki a gabansu na tabbatar da cewa duk wanda aka samu ya aikata wannan laifi ba kawai sun kama shi sun tsare ba ne, har ma a tabbatar an yi masa hukuncin da dika ta tanada ba tare da nuna son kai ba.
Da yake bayani kan wasu dabarun da masu almundahana a bankuna suke amfani da su, ya shawarci mutane su san yadda da yaushe da wanda za su ba shi labari kan harkokin kasuwancinsu ko harkokin da suka shafi rayuwarsu, wadanda a cewarsa suna iya bi ta hannun masu tallafa musu ko danginsu.
A jawabinsa, wakilina Babban Bankin Najeriya, Alhaji Abdulahi Hassan, ya bayyana almundahanar da ake yi ta kafofin sadarwar zamani da harkar banki ta Intanet da sauran hanyoyn rayuwa da manyan laifuffukan da suka keta doka, inda ya kara da cewa hada hannu a tsakanin Hukumar NCC da bangaren bankuna wata hanya ce ta magance matsalar.