✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta kara sayo jiragen yaki 24

Jiragen za su shige gaba a ayyukan yaki na Sojin Saman Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta bayar da kwangilar sayo sabbin jiragen yaki guda 24 samfurin Leonardo M-346 domin su shige gaba wajen ayyukan sojin sama a Najeriya.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar cewa tuni gwamnatin ta amince da sayo jiragen masu injina bibbiyu, kuma an kammala duk abin da ya kamata na kawo rukunin farko da ya kunshi 12 daga cikin jiragen zuwa kasar.

Kafar Humangle mai yada labarai ta intanet ta nakalto Daraktan Tsaron Rundunar Sojin Sama, Ashibel P. Utsu yana sanar da hakan a ranar Alhamis, yana mai cewa sabbin jiragen na da karfin yaki da leken asiri daga nisan zango daban-daban a sararin samaniya.

Ya bayyana cewa sayo sabbin jiragen na daga cikin matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka a yankurinta na maye gurbin jiragen yaki kirar Alpha Jet a matsayin jagora a cikin jiragen da Rundunar take amfani da su a fagen daga a halin yanzu.

Daraktan Tsaron ya sanar da hakan ne a bayanansa kan yunkurin gwamnati na kara yawan jiragen yakin Rundunar, bayan haska wani fim din Rundunar a ranar Alhamis, inda a ciki aka nuna nau’o’in jiragen yakin na M-346.

A cikin fim din, an nuna wasu sabbin jiragen na M-346FA, tare da nuna cewa Rundunar za ta koma amfani da su.

Babu tabbacin ko sabuwar odar da gwamnatin ta bayar za ta shafi shigo da ragowar jiragen yaki samfurin JF-17 Thunder da ta yi wa Rundunar, aka riga aka shigo da guda uku a matsayin rukunin farko.

Shigo da jiragen Leonardo M-346 din zai ba Rundunar Sojin Sama ta  Najeriya damar janje jiragenta na Alpha Jet daga fagen yake, ko ta mayar da su na bayar da horo.

– Jiragen yaki a Najeriya

A shekarun 1980 Gwamnatin Tarayya ta fara sayo jiragen Alpha Jet masu daukar mutum biyu guda 24, daga baya a 2015 zuwa 2018 ta sayo karin guda uku.

A shekarun baya-bayan nan jiragen na Alpha Jet ne ke kan gaba a ayyukan soji daban-daban da Najeriya ke yi a ciki da wajen kasar.

Suna aiki tare da jiragen yaki kirar F7-NI wadanda a halin yanzu ake gyaran su, da kuma jiragen L-39ZA Albatros da suma daga baya aka mayar na yaki.

– Jiragen yaki da Najeriya ta rasa

A baya-bayan nan, Najeriya ta yi asarar wasu daga cikin jiragenta na Alpha a bakin aiki, ciki har da wasu guda biyu da aka rasa a watannin Maris da Yuli na 2021.

A watan Satumba 2014, daya daga cikinsu da ke yaki da Boko Haram ya fado a Dajin Sambisa, inda kungiyar ta kashe daya daga cikin matukansa, daya kuma har yanzu ba a san inda yake ba.

A watan Mayun 2013, daya daga cikin jiragen da aka girke a Jamhuriyar Nijar ya yi hatsari.