✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta hada kai da Sao Tome don magance matsalar tsaro

Za a ci gaba da tunkarar matsalar fashin teku da sauran nau’o’in aika-aika a cikin ruwan gabar tekun Guinea.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ce rundunar sojin kasar nan za ta hada kai da takwararta ta kasar Sao Tome And Principe domin magance matsalolin tsaro musamman wadanda ake fuskanta a gabar tekunan da suka yi kasar iyaka.

Janar Irabor ya ce hadin kai tsakanin mayakan kasashen biyu na da tarin alfanu musamman wajen tunkarar kalubalen tsaro irin na zamani da ke faruwa.

Janar Irabor ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Sao tome and Principe, Janar Idalecio Pachire da ya ziyarci Hedikwatar Tsaro ta Kasa (DHQ) da ke Abuja.

Bayanai sun ce Janarorin biyu sun tattauna batun kalubalen tsaro a gabar tekun Guinea da irin rawar da kasashen biyu ke takawa.

Haka kuma Janar Irabor ya sha alwashin ci gaba da tunkarar matsalar fashin teku da sauran nau’o’in aika-aika a cikin ruwan gabar tekun Guinea.

Sauran hanyoyin da kuma sojojin kasashen biyu za su maida hankali su ne wajen horas da dakarun kasar Sao Tome, atisayen hadin gwiwa da sojojin Najeriya da sauran nau’o’in tallafi ga rundunar sojin kasar ta Sao Tome.

Baya ga Babbar Hedikwatar Tsaro da Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Sao Tomen Janar Pachire kazalika ya ziyarta, ya kuma ziyarci Hedikwatar Sojojin ruwan Najeriya da Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta rundunar sojin kasar.

Najeriya da Sao Tome dai sun dade suna da tarihin kyakkyawar alakar Diflomasiyya da na sha’anin tsaro da ya dauki she karu masu yawa.