✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta amince da amfani da riga-kafin cutar Maleriya

Da haka Najeriya ta zama kasar Afirka ta biyu da ta amince da riga-kafin Maleriya mai suna R21

Gwamnatin Najeriya ta amince a fara amfani da allurar riga-kafin zazzabin Maleriya wanda Jami’ar Oxford da ke Birtaniya ta samar.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC) ce ta ba da izinin amfanin da riga-kafin mai suna R21, duk da cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauransu ba su kammala bincike kan rashin hadarinsa ga dan Adam ba.

Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, ta sanara  ranar Litinin cewa, “An ba da izinin amfani da riga-kafin Maleriya mai suna R21 bisa tsarin da WHO ta tanadar.”

Da haka Najeriya ta zama kasa ta biyu a nahiyar Afirka da ta amince da riga-kafin, bayan kasar Ghana.

Sai dai duk da haka Shugabar NAFDAC din ta jaddada muhimmancin kammala binciken da ake gudanarwa a Najeriya kan riga-kafin cutar.

Cutar Maleriya wadda cizon sauro ke haifarwa na kashe sama da mutum dubu dari shida a duk shekara, akasarinsu kananan yara da mata ne a nahiyar Afirka, in ji WHO.

Rahoton WHO ya nuna a shekarar 2021 Najeriya ce kasar da ke dauke da kashi 27% na masu maleriya da kuma kashi 32% na wadanda ta yi sanadin mutuwarsu a duniya.

Yanzu dai babu tabbacin lokacin da za a fara amfani da riga-kafin R21 a Najeriya da Ghana, kuma har yanzu hukumomin duniya, ciki har da WHO na ci gaba da bincike kan nagartarsa da amincinsa ga jikin dan Adam.