✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ba irin su Atiku ko Tinubu take bukata ba a 2023 – IBB

Tsohon shugaban mulkin soja ne Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ba irinsu tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ko jagoran APC, Bola Tinubu…

Tsohon shugaban mulkin soja ne Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ba irinsu tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ko jagoran APC, Bola Tinubu kasar ke bukata su jagoranceta a 2023 ba.

Tsohon Shugaban ya ce kasar ta fi bukatar mai jini a jika, wanda bai wuce shekara 60 ba ya shugabance ta.

IBB ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a.

Ko da yake Tinubu da Atikun ba su fito karara sun bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023 ba, kwararan alamu na nuna cewa suna da sha’awar yin hakan.

Atiku dai shi ne ya yi wa jam’iyyar PDP takara a zaben da ya gabata, amma ya yi rashin nasara a hannun shugaba Buhari na APC.

Kazalika, shi ma Tinubu dukkan alamu sun nuna cewa zai tsaya takarar la’akari da yadda yaranshi suka rika kewaya sassan kasar nan don tallata shi.

To sai da IBB ya shaida wa gidan talabijin din na Arise cewar ya yi amannar dan kasa da shekara 60 ne zai fi dacewa da Najeriya.

Ya ce akwai akalla mutum uku da yake tunaninsu a yanzu haka.

Yanzu haka dai shekarun Atiku 75, kuma zai cika 77 nan da 2023 kenan, yayin da shi kuma Tinubu yanzu yake da 68, zai cika 70 daidai a lokacin.

IBB ya ce, “Tuni na fara harsashen shugaba na gari ga Najeriya. Shi ne irin shugaban da ya zaga lungu da sakon kasar kuma yake da jama’a a ko ina, duk inda ya je ya san akalla mutum daya.

“Irin mutumin da ya lakanci tattalin arziki, gogaggen dan siyasa wanda zai iya yin magana da ’yan Najeriya kai tsaye, da dai sauransu.

“Na ga kusan mutum daya zuwa biyu ko ma uku da suke da irin wannan da kuma basu wuce shekara 60 ba,” inji IBB.