✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAHCON ta sanya N2.8m a matsayin kudin kujerar Hajjin 2023

Farashin ya kasu gida takwas, inda jihohin Borno da Yobe za su biya mafi sauki

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta sanya Naira miliyan 2.88 a matsayin mafi karancin kudin kujerar aikin Hajji bana.

Aminiya ta ruwaito cewa bana an samu karin Naira dubu dari a farashin kujerar Hajji idan aka kwatanta da na shekarar 2022.

Shugaban Juna NAHCON, Zikrullah Hassan, ya ce an samu karin farashin ne sakamakon hauhawar farashin kaya a Najeriya da kuma faduwar darajar Naira.

Ya bayyana cewa a ranar 21 ga watan Mayu, 2023 za a fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Kasa Mai Tsarki.

Ya bayyana cewa farashin kujerar ya kasu gida takwas, inda jihohin Borno da Yobe da Adamawa za su biya mafi karanci, Naira miliyan 2.89.

Jihohin Legas da Ogun da Oyo za su biya mafi tsada a kan Naira miliyan 2.99 a yayin da sauran jihohin Kudu za su biya daga Naira miliyan 2.88 zuwa miliyan N2.99.

Zikrullah ya bayyana cewa dalilan bambancin kudin kujerar sun hada da yanayin  masauki da jihohi suka kama wa maniyyatansu; sannan kuma jihohin Arewa sun fi kuanci da Saudiyya a kan jihohin Kudu.

Ya bayyana cewa za a rufe shafin tsarin adashin gata na biyan kudin aikin Hajji a ranar 21 ga watan Afrilu, 2023.

Ya ce kamfanonin jiragen sama da aka amince su yi jigilar alhazan jihohi su ne Aero Contractors da Air Peace da Azman Air da da Fly Nas.

Wadanda za su yi jigilar ’yan jirgin yawo kuna su ne Arik Air da Value Jet.