✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Nagartaccen shugaba Najeriya ke bukata’

Ya kara da cewa sun zabi Gwamnan ne duba da kwarewarsa a tsarin mulki tun daga kasancewarsa Sanata zuwa Minista zuwa Gwamna.

Matasa masu neman Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya tsaya takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP (BAM-V) sun ce kasar nan na bukatar shugaba wanda zai cire wa mutanen kasar kitse a wuta.

Shugaban kungiyar na Jihar Nasarawa, Abubakar Usman Baba ne ya bayyana haka a lokacin kaddamar da kungiyar reshen jihar Bauchi wanda ya gudana a Monyi Hotel dake Lafiya.

Ya ce kungiyar BAM-V ta dubi ’yan takarar Shugaban Kasa da suka fara nuna sha’awarsu ta tsayawa takara, inda ta tankade su sannan ta gano cewa Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya cancanci ya jagoranci kasar nan zuwa ga tudun mun tsira.

“Saboda haka ne mambobin tafiyar nan reshen Jihar Nasarawa ta shiga sahun takwarorinta na jihohin Najeriya wajen kira ga Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi da ya fito ya tsaya takarar Shugaban in kasar nan a shekarar 2023,” inji shi.

Ya kara da cewa sun zabi Gwamnan ne duba da kwarewarsa a tsarin mulki tun daga kasancewarsa Sanata zuwa Minista zuwa Gwamna.

“Najeriya na fuskantar matsaloli da dama. Don haka ne muke bukatar shugaba da zai iya magance mana wadannan matsaloli. Muna da yakinin Gwamna Bala Mohammed yana da duk abin da ake bukata domin wannan aiki.”

A lokacin kaddamar da kungiyar reshen jihar Nasarawa dai, shugaban kungiyar na kasa, Kwamrade Mohammed Abubakar Jibo ya bukaci mambobin kungiyar su jajirce wajen nemo wa kungiyar tarin magoya baya domin su samu nasara.