✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na ji dadin aiki da Bankin Duniya —Dankwambo

Tsohon gwamnan ya ce a shirye ya ke don a sake damawa da shi a yanzu.

Tsohon gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya ce ya ji dadin aiki da Bankin Duniya ya ba shi aiki da kuma koyarwa da ya ke yi a wasu jami’oi uku na kasar nan.

Dankwambo wanda ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019, ya bayyana hakan ne yayin wata tarba da ‘ya’yan jami’yyar PDP suka shirya masa yayin dawowarsa Gombe, yana mai cewa a yanzu ya dawo domin a dama da shi a siyasa.

Ya ce da ya dauka mutanen Gombe sun manta da shi amma bisa ga wannan tarya da aka y masa, ya gane har yanzu ana maraba da shi.

Da ya ke bayani bayan kammala taron nasu, ya ce yanzu haka a shirye yake da ya sadaukar da kansa don mutanensa wajen yin takara don ba da gudumawarsa.

Ya kara da cewa, kamar yadda a 2019 ya yi takarar kujerar shugaban kasa yanzu idan jama’arsa suka ce ya sake tsayawa zai tsaya, idan kuma suka ce ya nemi wata kujera zai nema don tsige gwamnatin da ke mulki a Gombe.

Ya kuma ce ya dawo gida kenan ba zai tafi ba har sai sun karya gwamnatin APC, don haka duk wani dan PDP ya kwantar da hankalinsa yanzu za a yi siyasa.

Kazalika, ya jinjina wa al’umma kan yadda suka nuna masa goyon baya, suka tarbe shi saboda murnar dawowarsa gida bayan shafe shekara uku yana aiki da Bankin Duniya.