✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na cika alkawuran da na daukar wa ’yan Jigawa — Gwamna Badaru

Gwamnan ya ce ya cika alkawuran da ya dauka a 2015.

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce ya cika kaso 94.8 cikin 100 na alkawuran da ya daukar wa al’ummar jihar yayin yakin neman zabensa.
Badaru ya bayyana haka ne yayin bikin karrama shi da Inuwar Al’ummar Masarautar Hadeja ta yi a ranar Litinin, a Karamar Hukumar Hadeja.
A cewar Gwamnan, “Mun yi ayyuka da dama ciki har da wadanda ba a bukaci mu yi su ba, saboda haka mun cika kaso 94.8 cikin 100.
“Saura shekara daya ta rage mana, don haka za mu yi kokarin cikasa ragowar adadin da ya rage tare da karin wasu ayyukan,” a cewarsa.
Ya ce jama’ar yankin sun bukaci aiki guda 35 a lokacin yakin neman zabensa, kuma ya cika musu alkawari inda ya yi musu 33 daga cikin adadin da suka bukata.
Kazalika, Badaru ya gode wa masarautar Hadeja da al’ummar garin kan yadda suka karrama shi.
Da ya ke nasa jawabin shugaban inuwar, Baidi Muhammad, ya gode wa Gwamnan kan yadda ya dukufa wajen cika alkawuran da ya dauka.
Muhammad ya ce a 2014 jama’ar yankin na fama da matsalolin ayyuka da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum, amma gwamnan ya yi kokarin magance musu matsalolin tun bayan hawansa mulki a 2015.