✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mutuwar ‘ya’yana sojoji 2 a yakin Boko Haram ya jefe ni a kunci’

Wata matar aure mai suna Malama A’isha Umar wacce aka fi sani da Indo tana daya daga cikin iyayen da suka rasa ’ya’yansu sojoji a…

Wata matar aure mai suna Malama A’isha Umar wacce aka fi sani da Indo tana daya daga cikin iyayen da suka rasa ’ya’yansu sojoji a rikicin Boko Haram.

Malama A’isha mai kimanin shekara 45 da yanzu take zaune a gidan iyayenta a Unguwar Dandinshe a Karamar Hukumar Dala a birnin Kano sakamakon jinyar ciwon ido, ta ce kasancewar suna zaune a garin Jaji a Jihar Kaduna inda barikin sojoji yake ya sa yawancin matasa kan tashi da son shiga aikin soja. “Ni ma’ ya’yana biyu sai suka shiga aikin soja da Mubarak Hassan da Abubakar Hassan. Shi Mubarak yana aiki a Kaduna yayin da Abubakar  Jihar Abiya. Sai aka tura Mubarak zuwa Maiduguri. Ya zauna a can  kimanin shekara biyu kafin ya fara rashin lafiya. Ba mu san cewa ba ya da lafiya ba sai da rashin lafiyarsa ya yi tsanani. Shugabansu ya kira ni a waya ya sanar da ni halin da ake ciki ya kuma nemi mu je mu gan shi. Saboda dare ya yi sai muka yi niyyar zuwa da safe. Sai dai da yake Allah Ya raba ganawarmu gari na wayewa aka bugo mana waya cewa ya cika,” inji ta.

Ta kara da cewa: “Ganin yadda na rasa Mubarak a Maiduguri, ga shi dayan ma zai tafi, sai hankalina ya tashi. Amma sai shi Abubakar ya karfafaf min gwiwa cewa kowa idan kwanansa ya kare zai mutu. Kuma ya shaida min cewa sau biyar ana sa sunansa amma shugabansa yana cirewa. Amma a wannan karon dole sai ya je. Da zai tafi ya kira ni na yi masa addu’a. Watansa hudu a can ya samu dama ya zo gida ya ganmu. Bai cika wata uku da komawa Maiduguri ba ya rasu lokacin da wani bam ya fashe a Sabon Garin Dambuwa.”

“Kwana uku kafin rasuwarsa ya yi amfani da wayar abokinsa ya kira ni inda ya nemi a tura masa bashin kudi zai sayi waya kafin a biya su albashi. Muna cuku-cukun hada kudin da za a tura masa ne muka fara jin rade-radin cewa ya rasu kafin aka sanar da mu a hukumance,” inji ta.

A cewarta har zuwa yanzu idan ban da kudin binne gawa da aka biya na su biyun Naira dubu 500, ba a bin da ya sake biyo baya duk  da kokarin da mahaifinsu yake yi wajen bibiyar hakkokinsu.

“Mahaifinsa ya je wajen manyan sojojin da ya sani ya kai korafi, duk inda ya je za a nemi ya kai takadunsu da fasfonsu amma har yanzu bukata ba ta biya ba.  Ko kwanan nan ma an kira su a Abuja amma ba mu sake jin wani labari a kan lamarin ba,” inji ta.

Game da yadda ta samu ciwon ido, cewa ta yi, “Wani lokaci na tashi na ji idona yana ciwo ga kuma zazzabi mai zafi sai na je shagon magani aka ba ni magani. Bayan na ji sauki sai na fuskanci ba na gani da idona na bangaren dama. Hakan ya sa na je wani asibiti mai zaman kansa da ke Tudun Wada a Kaduna inda aka tabbatar min cewa hawan jini ne. Sai shi ma daya idon ya fara ciwo, sai likita ya nemi in je Asibitin Ido na Kasa da ke Kaduna inda aka ci gaba da ba ni magani. A duk lokacin da na je ganin likita nakan sayi magani daga Naira 7000 zuwa  8000. Amma duk da maganin da nake sha a kullum ganina raguwa yake yi. Duk da haka suka ce sai dai in ci gaba da sayen magani ba za a yi min aiki ba, har na daina gani. Da na ga haka sai na dawo wajen iyayena a nan Kano, inda muka ci gaba da neman magani a Asibitin Ido na Mishan. Duk lokacin da na je asibitin nakan sayi maganin sama da Naira dubu 10,” inji ta.

Malama A’isha ta nemi hukuma da masu hannu da shuni su kai mata dauki game da halin da take ciki, “Kin ga dama yaran nan su ne masu taimakona, tunda na rasa su rayuwata ta shiga wani hali, musamman rashin kudin magani. Maigidana ba ya da karfi haka iyayena ba su da halin da za su dauki dawainiyar biyan kudin aiki da na magani. Ni kuma a yanzu haka ba na iya gudanar da kowace irin sana’a sakamakon halin da nake ciki. Don haka nake rokon gwamnati ko wani mai hannu da shuni ya tallafa a dauki nauyin yi min magani domin yanzu haka an samu wani asibiti da ake gudanar da aikin irin ciwon idanuna, amma ba ni da halin zuwa,” inji ta.