✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar Sarauniya Elizabeth II: Me zai biyo baya?

An shirya liyafa saboda manyan baki da shugabannin kasashe da za su halarci jana’izar Sarauniyar.

Rasuwar Sarauniyar Ingila ke da wuya, sai mulkin ya koma kan danta wanda shi ne magajinta Charles, tsohon Yariman Wales, ba tare da wani bikin nadin sarauta ba.

Mutuwar Sarauniya Elizabeth ta sa an soma aiwatar da wasu tsare-tsare da za a bi daki-daki wadanda aka tsara dalla-dalla tsawon shekaru gabanin mutuwarta.

Zuwa yanzu dai babu wasu cikakkun bayanai dangane da yadda tsare-tsaren suke ko yadda za su kasance, sai dai ga wasu kadan daga cikin abubuwan da aka tabbatar za su bayyana a kwanaki masu zuwa.

Juma’a, 9 ga Satumba

A ranar Juma’a wadda ita ce rana ta farko bayan mutuwar Sarauniya, sabon Sarki Charles da matarsa Camilla wadda a al’adance ake kira Sarauniya Consort suka koma Landan.

Ana sa ran akwatin gawar Sarauniya Elizabeth wanda aka yi wa kawa da kuma lullubi da Tutar Masarautar Ingila zai ci gaba da kasancewa a gidan iyalan masarautar na Balmoral da ke Scottland, inda a nan ne ta cika.

A Yammacin Juma’ar ce Sarki Charles III na ya yi wa yan kasa jawabinsa na farko a matsayin Sarki wanda aka yada a kafafen talabijin na kasara.

An yi ta harbin bindiga a Hyde Park da Hasumayar Landan da kuma a cikin jiragen ruwa na yaki, sannan kuma aka karanta sanarwar ayyana Charles a matsayin Sarki a Edinburgh da Cardiff da Belfast.

Sabon sarkin ya yi zaman majalisa na farko da Firaiminista Liz Truss.

Kararrawar coci-coci a fadin kasar za su yi ta amsa amo, yayin da Cocin Ingila ya bai wa majami’u kwarin gwiwa bai wa mutane damar gudanar da addu’o’in musamman ga wadanda suke da sha’awar nuna alhini a wuraren bauta.

Firaminista da manyan ministoci sun halarci wani taron adduoi a Cocin St Paul wadda aka sadaukar ga marigayiya Sarauniya Elizabeth.

An bude wani littafi a Intanet domin jama’a su wallafa sakonninsu na alhini da ta’aziya.

Asabar, 10 ga Satumba

Abu na farko  daga cikin tsare-tsaren da za a gudanar na tsawon kwanaki goma bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth shi ne Majalisar Nadin Sarki da ake kira Majalisar Accession za ta ayyana Charlse a matsayin sarki.

Za a yi ta ’yan kade-kade da bushe-bushen sarewa yayin ayyana sabon sarki wanda bisa al’ada aka saba gudanarwa a Fadar St. James Park da ke Landan, sai kuma ayyanawar ta yadu a duk fadin kasar.

A wajen taron ayyana sarki, shugaban majalisar masarautar Dan Majalisa Penny Mordaunt ne zai sanar da rasuwar Elizabeth, kuma zai karanto wata sanarwa a bayyane cikin daga murya.

Kalaman sanarwar ka iya sauyawa, amma a al’adance dai jerin addu’o’i ne da alkawura da yaba wa mulkin sarauniyar tare da alkawarin goyon bayan sabon sarki.

Daga nan sai manyan jami’ai da suka hada da firaminista da Archbishop na Cocin Canterbury da kuma Shugaban Majalisar masarautar su sanya hannu.

Bayan duk wadannan matakai, za a mayar da hankali wajen gyara duk wani abu da aka cire ko aka kara ko aka sabunta, a matsayin wata alama ta sabon zamani.

Daga nan kuma Earl Marshal, wani babban jami’i daga cikin Majalisar Accession zai gana da kafafen yada labarai kan yadda taron ayyana sarkin ya wakana.

Ranar Lahadi, 11 ga Satumba

Za a dauke akwatin gawar Sarauniya Elizabeth daga gidan iyalan masarauta na Balmoral zuwa Fadar Holyrood da ke Edinburgh.

Wannan ’yar gajeriyar tafiya a al’adance ana ratsawa ta kananan garuwa da kauyuka domin bai wa al’umma dama ta farko su yi bankwana da Sarauniya.

A Scotland dai ana yi wa bikin jana’izar Sarauniya lakabi da ‘Operation Unicorn’ – Unicorn wata dabba ce da ba ta da wani bambanci da doki amma da tana da kaho guda daya a tsakiyar kanta tsakanin kunnuwanta biyu – wadda ita ce tambari ga kasar da ke nuna aminci.

Ranar Litinin, 12 ga Satumba

A wannan rana ce Sarki Charles zai soma wani rangadi da ake kira ‘Spring Tide’ a Ingila, Scotland, Wales da kuma Ireland ta Arewa – kasashe hudu na Birtaniya.

Za a sahu-sahu da tattaki wajen dauke akwatin gawar Sarauniya Elizabeth II daga Fadar Holyrood Abeey da ke Edinburgh zuwa Cocin St Giles, inda za a shafe dare ana addu’o’i wanda kuma iyalan gidan sarauta za su halarta.

Ranar Talata, 13 ga Satumba

Za a mayar da akwatin gawar Sarauniya zuwa babban birnin kasar a jirgi, sannan kuma a sake daukarsa a mota zuwa Fadar Buckingham da ke Landan.

Mazauna birnin za su yi sahu-sahu a gefen hanya na duk wasu tituna da za a ratsa yayin wucewa da gawarta.

Ranar Laraba, 14 ga Satumba

Za a yi wani kwarya-kwaryan biki a Landan wanda aka yi wa lakabi da ‘Operation Feather’, inda a za ajiye akwatin gawar Sarauniya a Zauren Majalisa da ke Westminster.

Manyan iyalan gidan sarauta za su tsaya su kewaye akwatin gawar wanda aka saba ala’adance kuma ake kiran hakan ‘Vigil of the Princes’.

Ranar Alhamis, 15 zuwa Asabar, 17 ga Satumba

A tsawon kwanakin za a ajiye akwatin gawar Sarauniya inda jama’a za su yi ta tururuwa suna wucewa domin girmamawa da kuma bankwana da ita.

Ranar Lahadi, 18 ga Satumba

Za a shirya liyafa saboda manyan baki da shugabannin kasashe da za su halarci jana’izar Sarauniya.

Ranar Litinin, 19 ga Satumba

Dubban mutane za su taru a tsakiyar birnin Landan yayin da za a gudanar da jana’izar Sarauniyar a Westminster Abbey.

Manyan iyalan gidan sarauta za su yi sahu-sahu a bayan akwatin gawar wanda za a dauko wani amalanke inda za a yi shiru na tsawon minti biyu.

Bayan nan ne za a mayar da gawar zuwa Cocin St George da ke gidan sarauta na Windsor Castle, wanda za a nada a gidajen talibin.

Daga nan kuma zuwa a kai gawar makwancinta na karshe, inda za a binne ta a Cocin Sarki George VI – a gefen kabarin mijinta, Yarima Philip, da tokar yar uwarta, Gimbiya Margaret, da Mahaifyarsu kuma takwararta, Elizabeth da kuma mahaifinsu, Sarki George VI.