✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutuwar Attahiru: An bukaci garambawul a sufurin jiragen saman soji

Mutuwar Attahiru abin takaici ne saboda ya kai kololuwa a aikinsa na soji.

Wasu masana harkar tsaro sun nuna alhininsu game da mutuwar manyan hafsoshin soja a hadarin jirgin sama tare da yin kira da a sake nazari sosai game da bangaren sufurin jiragen saman soja.

Aminiya ta ruwaito cewa Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojin guda 10, sun mutu a hadarin jirgin saman ranar Juma’a a Kaduna.

Masana harkar tsaro sun fada wa Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya, NAN, a tattaunawa daban-daban a ranar Lahadi cewa faruwar lamarin koma baya ne ga ci gaban tanadin kasar a yakin da take yi da masu tayar da kayar baya.

Manajan Darakta na wani Kamfanin Tsaro, Mista Chinye Bones, ya ce akwai bukatar sake duba bangaren jiragen sama na soja domin hana aukuwar irin wannan mummunan lamarin a nan gaba.

Ya ce an sami raguwar hadarin jiragen saman fasinja bayan an yi wa bangaren garambawul a lokacin mulkin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.

“Ya bayyana damuwa ne kwarai kan yadda hadarurruka ke faruwa a bangaren sufurin jiragen saman soja; kuma abin takaici shi ne wani babban hafsan soja ya rasa ransa ta dalilin haka.

“Wannan ya nuna matukar lalacewa da jiragen saman sojojinmu suke fuskanta har ta kai ga jirgin da zai dauki Babban Hafsan Sojin Kasa na iya faduwa har ya kama da wuta.

“Attahiru ya mutu ne kawai sakamakon rashin kulawa ko zagon kasa da wasu marasa kishi suka yi,’’ inji Bone.

Don haka, ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faduwar jirgin ta yadda za a kiyaye aukuwar hakan a nan gaba.

“Ina mika ta’aziyyata ga iyalan mamatan tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon jure rashin da suka yi.’’

Haka nan, Mista Dennis Amachree, wani masanin harkokin tsaro, ya ce lamarin ya faru ne lokacin da ‘yan Najeriya ke dakon ganin sababbin dabaru da sabon Babban Hafsan Sojin Kasan zai bullo da su a yaki da tayar da kayar baya.

Amachree ya ce mutuwar Attahiru abin takaici ne saboda ya kai kololuwar aikinsa bayan ya kwashe shekaru da dama yana bauta wa kasarsa.

“Ya mutu a bakin aiki kuma wannan ba karamar illa ba ce ga sojojin, musamman a yakin da suke yi da ta’addanci.

“Duka Sojojin Najeriya da sauran rundunonin sojojin kasar baki daya za su yi kewarsa sosai kuma ina mika ta’aziyata zuwa ga danginsa,’’ inji shi.

Hakazalika, Ben Okezie, shi ma masanin tsaro ya ce ya kamata gwamnati ta himmatu wajen kula da iyalan da sojojin da suka mutu suka bari.

“Sun mutu yayin da suke yi wa kasar aiki tukuru kuma dole ne al’umma ta girmama gudummawar da suka bayar da kuma sadaukar da kansu ga ci gaban rundunar sojin Najeriya,’’ inji Okezie.

Ya kuma yaba wa marigayi Attahiru, wanda a cewarsa, ya nuna shugabanci wanda ‘yan Najeriya ke matukar so.

“Sunansa zai shiga tarihi a matsayin jarumin soja wanda ya mutu a hidimtawa kasarsa.

“Allah Ya sa ya huta cikin kwanciyar hankali kuma Allah Ya ba wa danginsa kwarin gwiwar jure rashin.’’

Wani tsohon kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Legas, Mista Fatai Owoseni, ya jajantawa dangin Babban Hafsan, ya kara da cewa mutuwarsa sakamakon hadarin jirgin saman soja abin bakin ciki ne.

“Me kuma za a ce fiye da fadin wannan wani lamari ne na bakin ciki, babban rashi ga danginsa da kuma Najeriya.

“Ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa iyalansa kwarin gwiwar jure rashin,’’ inji Owoseni.

Mista Benjamin Esegine, masanin tsaro, ya kuma bayyana lamarin a matsayin wani abin takaici.

Esegine ya ba da shawarar cewa ya kamata Najeriya ta mai da hankali sosai wajen kula da jiragen sama na soja da na farar hula.

“Wannan lamari ne mara dadi kuma na yi matukar bakin ciki saboda mutuwa ce da za a iya guje wa.

“Allah Ya jikan wadanda suka mutu Ya sa sun huta.

“Amma, wannan ya wuce mu tsaya ga addu’a kadai; lallai ne mu yi hobbasa ta yadda ba za mu jira har sai wannan bala’in ya koma zuwa jiragen sama na kasuwanci.

“Gyaran jiragen sama yana da muhimmanci kasancewar rai fa guda ne. Wannan abin bakin ciki ne,’’ inji shi.