✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutumin da ke kai wa ’yan bindiga abinci da fetur ya shiga hannu a Kano

Wanda ake zargin ya fito daga garin Jibiya ne na Jihar Katsina.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani mutum da ake zargi da kai wa ’yan bindigar Katsina abinci da man fetur a Karamar Hukumar Fagge, da ke cikin birnin Kano.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan inda ya ce an cafke shi tare da wani direban mota kirar J5, dauke da man fetur da buhunan kayan abinci.

Wanda ake zargin na da shekara 31 a duniya, shi kuma direban motar na da shekara 37, dukkansu ’yan asalin garin Jibiya ne ta Jihar Katsina.

Kakakin ya ce, “A ranar 15/10/2021 da misalin karfe 12:30 na rana, rundunar ’yan sanda karkashin jagorancin CSP Abubakar Hamma sun yi nasarar cafke wata mota kirar J5 tare da wasu mutum biyu dauke da kayan abinci.

“A yayin da ake bincikar motar, an gano jarkar man fetur lita 25 har guda biyar makare da man fetur, wanda aka batar musu da kama aka saka su cikin buhun sukari, sannan an cafke mutum biyun da ake zargi,” inji Kiyawa.

Kakakin ya kara da cewar, daya daga cikin wanda ake zargin ya amsa cewar ya fito ne daga garin Jibiya a Jihar Katsina, ya shigo Kano don sayan man fetur sannan ya koma inda ya ke sayar wa a farashi mai dan karen tsada.

Bugu da kari, kakakin ce wanda ake zargin ya sake amsa cewar wannan shi ne karo na biyu da ake cafke shi yana safarar man fetur din.

“Kwamishinan ’yan sandan Kano ya ba da umarnin zurfafa bincike don gano wasu bayanai, sannan kuma za a mika shi kotu da zarar an kammala,” cewar Kiyawa.

Har wa yau, ya ce Kwamishinan ya umarci al’ummar jihar da su farga tare da bada rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba a yankunansu ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.

Sannan ya shawarci masu gidajen man fetur da su guji sayar da man fetur mai yawa ga mutanen da ba su sani ba, sannan su mika rahoton duk wani wanda suke zargi zuwa ofishin ’yan sanda mafi kusa.