✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 4.3 za su fuskanci matsananciyar yunwa a jihohi 3 na Najeriya —MDD 

Za a fuskanci mummunar matsalar tamowa da mace-mace saboda karancin kai kayan agaji.

Shirin Majalisar Dinkin Duniya na Samar da Abinci WFP, ya yi gargadin cewa akwai mutum miliyan 4.3 da za su yi fama da matsananciyar yunwa a wasu jihohi uku na Najeriya.

A cewar shirin na WFP (World Food Programme), jihohin uku sun hada da Adamawa da Borno da kuma Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Shirin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, game da wani rahoto da ya tattara kan matsananciyar yunwa a yankin kasashen Kudu da Hamadar Sahara.

Shirin na WFP ya nuna damuwa kan rikicin da aka kwashe shekaru ana yi da ’yan bindiga zai iya jefa Najeriya cikin yunwa da tamowa.

Haka kuma, shirin ya ce wannan faruwa ne a yayin da miliyoyin mutane suka dogara kan taimako da ake ba su na abinci, wanda kuma suke fuskantar barazanar fadawa cikin yunwa.

“Kimanin mutum 600,000 na kan gabar fadawa cikin wannan musifa.

Mutane za su fuskanci yanayin neman daukin gaggawa saboda karancin abinci.

“Za kuma a fuskanci mummunar matsalar tamowa da mace-mace saboda karancin kai kayan agaji,” in ji shirin.