✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 93 ’yan bindiga suka kashe a kauyen Zamfara

Maharan da ke magana da yaren wata kasa sun harbe masu neman guduwa daga kauyen.

Mutum akalla mutum 90 ne aka kashe a harin da ’yan bindiga suka suka kai kauyen Kadawa na Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.

Wani mazaunin Kadawa mai suna Lawali ya ce gawa 67 ne aka gano a cikin kauyen, sai wasu 26 a da aka gano a wurare kusa da garin, baya ga mutane da dama da maharan suka harbe su.

Da yake tabbatar da harin a ranar Juma’a, kakakin ’yan sanda a Jihar Zamfara, SP Shehu Mohammed, ya ce, “Gaskiya ne an kai hari a kauyen Kadawa na Karamar Hukumar Zurmi, inda ’yan bindiga suka bi dare a ranar Alhamis suka yi wa mutane kisan gilla.”

Wasu shaidu a kuayen na Kadawa sun ce maharan na magana ne da wani yare da ba na Najeriya ba, kuma sun yi ta bin mutanen da suka yi kokarin tserewa daga kauyen suna harbewa.

“Bayan samun labarin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, CP Hussain Rabiu, ya tura rundunar hadin gwiwa zuwa yankin domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin jama’a da kuma kamo maharan su fuskanci hukunci.

“CP Hussain Rabiu da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Nasiru Magarya, sun kuma ziyarci kauyen domin yin ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu,” inji kakakin ’yan sandan.

Kafin bullar rahoton harin a ranar Juma’a, Gwamnan Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya bukaci al’ummomin jihar da su tashi su kare kawunansu daga hare-haren ’yan bindiga.

Da yake bayyana hakan a taron gudanar da addu’o’i na musamman kan cikarsa shekara biyu a kan mulki, Matawalle ya ce gwamnonin Arewa sun yi ittifakin kafa rundunar tsaro da matasa da za su rika taimaka wa jami’an tsaro a yankunansu.