Mutum 12,233 ne suka kamu da cutar coronavirus bayan kwana 100 da fara bullar annobar a Najeriya.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Nigerian (NCDC) ta sanar da haka a alkaluman da ta fitar ranar Asabar 6 ga watan Yuni da muke ciki.
Bayan kwana 100 NCDC ta tabbatar da sallamar mutum 3,826 da suka warke daga cutar, baya ga wasu 342 da ta yi ajalinsu a fadin kasar.
Wadanda cutar ta kama ko ta kashe sun kunshi ma’aikatan lafiya, manyan jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa, masana, dalibai, da mashahuran mutane da sauran bangarorin ‘yan kasar.
Alkaluman sun ce mutum 389 ne suka kamu da cutar daga jahohi 23 a ranar da bullar cutar ke cika kwana 100 a Najeriya.
Ya zuwa yanzu jiha daya ce tal a Najeriya ba a samu bullar cutar ba, kamar yadda bayanan NCDC suka nuna.
A breakdown of cases by state can be found via https://t.co/zQrpNeOfet#TakeResponsibility pic.twitter.com/n2MQeLTZLp
— NCDC (@NCDCgov) June 6, 2020
A ranar 27 ga watan Fabrairun 2020 ne NCDC ta tabbatar da bayyanar cutar a jikin mutum na farko a Najeriya —wani dan kasar Italiya da ya shigo Najeriya ta Legas a ranar 24 ga watan.
Bullar cutar wadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana a matsayin annoba ta duniya, a Najeria ta sa NCDC kara yawan dakunanta na gwajin cutar wadda mutum 8,065 ke fama da ita a halin yanzu.
A hankali cutar wadda ta samo asali a yankin Wuhan na kasar Sin ta rika yaduwa zuwa sassan Najeriya, lamarin da ya tilasta wa hukumomi da ma ‘yan kasa daukar matakan dakile yaduwarta.
Acikin kwana 100 dakunan gwajin COVID-19 na NCDC sun karu daga 3 zuwa 30 a fadin kasar da karfin gudanar da gwaje-gwaje 10,000 a kullum.
Kana yawan cibiyonyin killace masu cutar da na bayar da agajin gaggawa da kuma jami’ai da hukumomi masu aikin yaki da ita da kuma lura da yanayin yaduwarta ke ta karuwa a kasar.
Cikin kwana 100 a kalla ma’aikatan lafiya 13,000 NCDC ta ce an horas kan yaki da COVID-19.
Yanzu cutar COVID-19 ta kama mutum sama da miliyan 6 bayan bazuwar cutar zuwa kasashe fiye da 100 a fadin duniya.
Cutar ta kuma yi ajalin mutum sama da 300,000 a fadin duniya.
A Najeriya, NCDC ta ce za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomi uwin shawo kan cutar a fadin kasar.