✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3 sun mutu sakamakon fadan kabilanci a Ibadan

Rahotanni sun ce lamarin ya janyo kone-konen gidaje da shaguna mallakar bangarorin biyu.

Al’ummar Hausawa da ke zaune a birnin Ibadan na Jihar Oyo na cikin zaman dar-dar bayan barkewar fadan kabilanci tsakanin ’yan kasuwarsu da na Yarbawa, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka uku.

Rahotanni sun ce lamarin, wanda ya faru a kasuwar Sasa da ke Ibadan ya janyo kone-konen gidaje da shaguna da sauran kadarori mallakar bangarorin biyu.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa fadan na ranar Juma’a ya biyo bayan wata gardama da aka yi ne da yammacin ranar Alhamis a tsakanin wani lebura Bahaushe da wata mata Bayarabiya kan zubar da dagwalon shara da leburan ya yi a harabar shagonta.

Hakan ya haifar da ka-ce-na-ce tsakaninsu, har abin ya ta’azzara ya kai ga doke-doke.

Kokarin kare kansa da leburan ya yi ne ya kai ga naushin daya daga cikin Yarabawan mai suna Adeola Sakirudeen da ke tare da matar a lokacin inda ya fadi kasa a sume, kafin daga bisani a garzaya da shi Asibiti da aka tabbatar da mutuwarsa a daren ranar Alhamis.

Hakan ne ya sa daruruwan Yarabawa fitowa da sanyin safiyar ranar Juma’a domin mayar da martani da daukar fansa inda suka yi arangama da Hausawa masu kare kansu.

Da Aminiya ta ziyarci Kasuwar ta Sasa da misalin karfe 10:00 na safiyar Juma’a, ta gane wa idanunta irin yadda bangarori biyu na Hausawa da Yarabawa suka ja daga dauke da makamai kamar su adduna da wukake da sanduna da kwalabe suna jifan juna da duwatsu tare da kona gidaje da kantuna.

An farfasa gilasai da tayoyin manyan motocin da suka yi dakon kayan miya daga Arewa zuwa kasuwar ta Sasa.

Mahukumta sun yi hanzarin girke rundunar tsaron hadin gwiwar sojoji da ’yan sanda da Amotekun domin kwantar da rikicin, sai dai an ci gaba da kaurewa da fada a gaban wadannan jami’ai ba tare da daukar matakin hanawa ba.

Kwamishinar ’Yan Sandan Jihar Oyo, Uwargida Ngozi Onadeko tare da mai ba Gwamna Shawara a kan Harkokin Tsaro da wasu manyan jami’an gwamnati sun ziyarci kasuwar ta Sasa amma ba su kai ga shiga cikin dandalin fadan ba suka fice suka koma gidan Gwamnati domin isar da sakonsu ga Gwamna Seyi Makinde.

Sai dai Kakakin ’Yan Sandan Jihar Olugbenga Fadeyi ya tabbatar da aukuwar lamarin amma ya ce mutum daya ne kawai ya rasa ransa.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci gidan Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, ta taras da daruruwan tsofaffin mata da kananan yara sun cika gidan makil domin samun mafaka bayan kaurace wa gidajensu domin tsira da rayukansu.

A daidai wannan lokaci ne aka hango wasu matasan Hausawa da aka dauko su jina-jina da raunuka a jikinsu da aka garzaya da su zuwa asibiti.

Wasu daga cikin mutanen da suka tsere daga gidajensu sun tare ne a gidajen makwabta da wasu unguwannin Hausawa.

Binciken ya tabbatar da ci gaba da kaurewar fadan har zuwa cikin daren ranar Juma’a a inda mafi yawancin matasa Hausawa suka taru wuri daya a harabar kofar gidan Sarkin Sasa domin kare kansu zuwa wayewar garin ranar Asabar.

Yanzu haka farashin kayan miya kamar tumatir da tattasai da albasa ya fara tashi sama a birnin Ibadan da kewaye a dalilin barkewar wannan fada a Kasuwar ta Sasa da makwabtan jihohi ke rububin zuwa a kulluyaumin domin sayan irin wannan kaya.