✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 3 sun kone kurmus a hatsarin mota a Kano

Motar ta kone wasu fasinjoji uku mata kurmus.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce fasinjoji mata uku ne suka mutu yayin da wasu 13 suka samu raunuka a lokacin da wata motar haya bas ta kama wuta a ranar Talata.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.

Ya ce motar hayar kirar Toyota Hiace mai lamba XE 222 TRN ta kama da wuta ne a kusa da Kwalejin Fasaha ta Gwamnati da ke Karamar Hukumar Nassarawa ta jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne yayin da motar bas da ta fito daga Karamar Hukumar Ajingi zuwa Kofar Wambai ta kone kurmus.

Sanarwar ta ce jami’an kashe gobara da jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) sun yi nasarar kashe gobarar tare da samun nasarar ceto wasu fasinjojin.

Abdullahi ya ce wasu mata uku da ke cikin bas din sun kone ta yadda ba za a iya gane su ba; ya bayyana sunayensu a matsayin Surayya Umar da Zeenai Babaji.

Ya ce sauran 13 da suka samu raunuka an kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin yi musu magani.

Amma an ceto direban motar mai suna Muhammed Gali mai shekara 35 da kwandastansa, Hassan Danladi mai shekara 30 ba tare da wani rauni ba, aka mika su ga ’yan sanda don yin bincike.