✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mutum 23 ne ‘yan bindiga suka kashe a harin Zamfara’

Harin ‘yan bindiga ya kashe mutum 23 a yankin Ruwan-Tofa da ke jihar Zamfara ranar Asabar, a cewar mazauna. Harin shi ne mafi muni da…

Harin ‘yan bindiga ya kashe mutum 23 a yankin Ruwan-Tofa da ke jihar Zamfara ranar Asabar, a cewar mazauna.

Harin shi ne mafi muni da aka kai yankin cikin shekaru uku  tun da ‘yan bindiga suka fara kai hare-hare a jihar, inji wani mai taimaka wa gwamnan jihar, Mu’azu Yusuf.

Tun da farko dai rahotanni sun ce an kashe mutum 10 a harin na gundumar Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru ta jihar Zamfaran.

Mazauna sun ce daga baya wasu da suka jikkata a harin da aka kwantar a asibitin garin sun mutu, an kuma tsinci gawarwakin wasu da aka kashe a cikin dazuzzuka, lamarin da ya kara alkaluman zuwa 23.

Akalla mutum 10 ne ke kwance a asibitin Dansadau har yanzu suna karbar magani sakamakon raunukan da suka samu daga harin.

Jama’ar yankin sun ce sun sami labarin yunkurin kai harin kwanaki uku kafinsa sun kuma ankarar da jami’an tsaron da suka kamata cikin lokaci amma suka gaza yin abin da ya dace.

Yusuf ya nuna takaici cewa jami’an tsaro sun isa yankin ne bayan maharan sun gama cin karensu babu babbaka, yana mai cewa sun zo ne kawai su halarci jana’izar mamatan.

To sai dai kwamishinan tsaron jihar, Abubakar Dauran ya ce gwamnatin jihar ta jibge karin jami’an tsaro a yankin don hana sake kwararowar ‘yan bindiga daga jihohi makwabta.

Ya kuma musanta cewa mutum 23 ne aka hallaka a harin, yana mai cewa mutum 14 suka tabbatar.

Sai dai kwamishinan bai musanta cewa jami’an tsaron sun sami bayanan sirri kan harin tun kafin a kai shi ba kuma suka ki yin komai.