✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da za su wakilci Buhari a auren dansa Yusuf a Bichi

Tawagar dai za ta kasance karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Gambari.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike da wata kwakkwarar tawaga zuwa Jihar Kano da za ta wakilce shi yayin durin auren dansa Yusuf, da za a yi ranar Juma’a a Bichi.

Za a daura auren Yusuf ne, wanda shi kadai ne dan Buhari namiji da amaryarsa, Zahra, ’ya ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero bayan Sallar Juma’a a garin na Bichi da ke Jihar Kano.

Tawagar dai za ta kasance karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ranar Alhamis dauke da sa hannun, Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu.

A cewar sanarwar, tawagar ta kunshi Ministan Tsaro, Bashir Magashi da na Aikin Gona da Raya Karkara, Sabo Nanono da na Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika da kuma na Albarkatun Ruwa, Sulaiman Adamu.

Kazalika, Malam Garba Shehu shi ma zai kasance a cikin tawagar kuma zai tsaya har zuwa ranar Asabar domin wakiltar Shugaba Buhari a wajen bikin ba Sarkin Bichi sandar mulki.

Ana dai sa ran halartar Gwamnoni da ’yan siyasa da sarakuna da ’yan kasuwa da sauran muhimman mutane daga sassa da dama na Najeriya.

Rahotanni dai sun ce Shugaba Buhari zai kai ziyarar aiki ne Jihar Adamawa ranar Juma’a, inda tuni aka tsaurara matakan tsaro a can.