✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutane sun gudu daga kauyukan Abuja 8 saboda barazanar ’yan bindiga

Mata da kananan yara duk sun gudu, sai ’yan tsirarun maza

Mata da kananan yara sun gudu sun bar muhallansu a wasu kauyuka takwas da ke yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, bayan ’yan bindiga sun yi barazanar kai musu hari.

Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Adagba da Gurdi da Tekpeshe da Kutara da Rafin-Daji da Lafiya Yaba da Mayaki da kuma Gulida, dukkansu a karamar hukumar Abaji.

Lokacin da wakilin Aminiya ya ziyarci wasu daga cikin kauyukan, ya iske akasarin gidajensu sun kasance babu kowa a ciki, sai dai wasu ’yan tsirarun mutane da suka rage, akasarinsu maza a karkashin bishiyu, yayin da wasu suke aiki a gonakinsu.

Wani mazaunin Adagba wanda wakilin namu ya iske yana aiki a gonarsa, Yakubu Ibrahim, ya ce tilas ta sa ya kwashe matansa biyu da ’ya’yansa daga kauyen.

Ya kuma ce mutane da dama su ma sun kwashe iyalansu, shi kuma ya tsaya ne saboda gonarsa.

“Na kwashe iyalaina zuwa ’Yangoji. Ni ma ba na kwana a nan. Idan na kammala aikina, Yaba nake zuwa na kwana, sai da safe na sake dawowa,” inji Yakubu.

Dagacin kauyen na Adagba, Abdullahi Mayaki, ya tabbatar da yin hijirar mutane garin nasa, inda ya ce sun yi hakan ne saboda barazanar ’yan bindigar.

Dagacin ya ce, “Wasu daga cikin jama’ar garina sun tsaya bayan kwashe iyalansu zuwa Yaba da Abaji da ’Yangoji. Wata matsalar kuma da muke fuskanta ita ce ta yadda makiyaya ke amfani da damar wajen kado dabbobinsu suna cinye mana amfanin gona.”

Ya ce ’yan ta’addan sun aika wa mutanen garin sako ne ta hanyar mutanen da suka sace a Tekpeshe cewa su shirya suna nan tafe.

Kazalika, wakilinmu ya kuma ziyarci kauyukan Tekpeshe da Gurdi, inda a can ma ya iske ’yan tsirarun mutane.

Usman Aliyu, wani mazaunin garin Gurdi, ya ce mazauna yankin na cike da fargabar ayyukan ’yan bindiga.

Ya ce, “Kamar haka ne fa suka yi barazanar kai hari kauyen Zago da ke da makwabtaka da mu a jihar Neja, yanzu sun tashe shi gaba daya. Kai hatta Dagacin garin ma yanzu ya koma Abaji shi da iyalansa.”

Da wakilin namu ya ziyarci gidan Dagacin Gurdi, Alhaji Bala Mohammed, bai iske shi a gida ba, inda aka shaida masa cewa ya tafi Yaba, bayan Etsu na Yaban ya gayyace shi wani taro kan harkar tsaro a yankin.

Aminiya ta kuma gano cewa an sace mutum biyar a kauyen Zago da ke da matwabtaka da Gurdin, wanda kuma yake jihar Neja, a Larabar da ta gabata.

Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Neja, DSP Wasiu Abiodun, bai daga ko dawo da kiran wayar wakilinmu ba don jin ta bakinsu a kan wannan harin.

Ita ma Kakakin ’yan sandan Abuja, DSP Adeh Josephine, ba ta amsa sakon kar-ta-kwanan da wakilin namu ya tura mata ba a kai.