✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Musulmai 6 da ke yin wasan Wrestling

'Yan wasan shida kowa na da asalinsa da kuma yadda fara buga wrestling.

Wrestling ya kasance daya daga cikin wasanni da suka yi suna a duniya, hakan ya sa mutane da dama ke kaunar kallonsa.

Musulmai ma kamar kowa ba a barsu a baya ba; yayin da su ma suka tsunduma cikin wasan da ake yi walakabi da WWE.

Ga wasu musulmai 6 da suka yi fice a wasan:

1. Mansoor Al-Shehail: Mansoor Abdul Aziz Al-Shehail dan asalin kasar Saudiyya ne, Mansoor ya buga wasanni irin su Royal Rumble, Smack Down da sauransu.

Mansoor Al-Shehail
Mansoor Al-Shehail

2. The Iron Sheik: Hossein Khosrow Ali Vaziri, wanda ake kira da ‘The Iron Sheik’ tsohon dan wasan wrestling ne kuma dan asalin kasar Amurka amma yana da asali da kasar Iran. Musulmi ne mabiyin Shi’a kuma daya daga cikin ‘yan wasan wrestling da suka yi fice a zamaninsa.

The Iron Sheik
The Iron Sheik

3. Ariya Daivari: Kafin shigarsa wrestling Daivari, ya buga wasan kokawa irin su ‘Honor’ da ‘Global Force Wrestling’. Daivari shi ma musulmi ne kuma dan asalin kasar Amurka.

Ariya Daivari
Ariya Daivari

4. Sami Zayn: Rami Sebei, wanda aka fi sani da ‘Sami Zayn’ dan asalin kasar Canada ne kuma kwararren dan wasan wrestling. Shekaru takwas da suka gabata Zayn, ya zama zakaran WWE.

Sami Zayn
Sami Zayn

5. Muhammad Hassan: Marc Julian Copani, wanda ake wa lakabi da ‘Muhammad Hassan’ a wrestling, tsohon dan wasan wrestling ne kuma dan kasar Amurka. Sai dai dan wasan bai jima yana wasan wrestling ba, inda ya fara a 2004 sannan ya yi ritaya a 2005 ya koma malamin makaranta.

Muhammad Hassan
Muhammad Hassan

6. Mustafa Ali: Adeel Alam dan asalin kasar Amurka ne kuma ya yi fice tare da samun farin jini a wajen masu kallon wrestling. Kafin shigarsa WWE, Alam ya fara wasan wrestling a Criuserweight wanda daga nan ne ya zama gwarzo har ya samu kwantaragi da kamfanin WWE.

Mustafa Ali
Mustafa Ali