A makon jiya ne aka bayar da labarin wata bajinta da wani maigadi mai suna Malam Musa Usman ya yi, inda ya bukaci a samar wa al’ummarsa rijiyar burtsatse maimakon a gina masa gida.
Shi dai Malam Musa Usman mutumin kauyen Giljimoni ne wata ruga da ke Karamar Hukumar Birniwa a Jihar Jigawa. Ya bar kauyensu ya tafi Legas neman abinci inda ya zama maigadi a gidan shugaban wani kamfani mai suna Jawa International Limited, Shugaban Kamfanin Mista B. Berghese, wanda dan kasar Indiya ne. Ya ce Malam Musa Usman ya kwashe shekara 25 yana gadi a gidansa, kuma duk tsawon lokacin nan ba a taba samun wani abu da ya bace a gidan nasa ba. Ya kara da cewa, yakan yi tafiya zuwa kasarsu Indiya amma zai dawo ya tarar da gidansa lafiya babu abin da aka taba.
Mista Berghese ya kara da cewa, saboda jin dadin zama da ya yi da Malam Musa ne ya sanya da ya ce zai bar aiki bayan ya kwashe shekara 25 yana tare da shi, sai ya yanke shawarar ya gina wa Malam Musa gida a kauyensu domin nuna jin dadin zaman da suka yi da shi, amma sai Malam Musa ya ce shi ya fi so a samar wa al’ummar kauyensu rijiyar burtsatse domin a saukaka musu wahalar da suke fuskanta wajen samun ruwan da za su yi amfani da shi yau da kullum, saboda mutanen kauyen nasu suna fuskantar matsala wajen samun ruwa.
Shi da kansa Mista Berghese ya bayyana wannan sadaukarwar da Malam Musa ya yi a lokacin da yake jawabi a yayin kaddamar da rijiyar burtsatsen da ya samar a kauyen su Musa. Wannan ya sanya hankalin kowa ya koma kan Malam Musa Usman saboda wannan sadaukarwar da ya yi domin al’ummarsa su amfana, maimakon ya karbi abin da shi da iyalinsa kadai za su amfana.
Haka ake so mutane su zama, wato su rika fifita jama’arsu fiye da kawunansu, sabanin abin da ke faruwa a yanzu inda mafi yawan mutane ba su son taimaka wa al’umma, sai dai su kasance daga su sai ’ya’yansu kawai, kuma ba su son wani ya zama kamarsu, sun fi so kullum su kasance su ne a sama, wato su zama daban da sauran jama’arsu.
Malam Musa Usman bai zabi ya zama daban da sauran mutanen kauyensu ta hanyar kasancewa mai gidan da ya fi na kowa kyau a kauyensu ba. Maimakon haka sai ya zabi ya ci gaba da zama a gidansa na ciyawa amma da shi da mutanensa su samu ruwa mai kyau kuma ba tare da wahala ba.
Wannan sadaukarwar da ya yi ta daukaka darajarsa domin ta sanya ya yi suna a duniya inda kowa so yake ya gan shi, kuma sunan kauyensu ya shiga duniya. Sannan al’ummarsa ba za su taba mantawa da karamcin da ya yi musu ba.
A duk lokacin da aka dibi ruwa a wannan famfo, Malam Musa yana da lada, har bayan mutuwarsa zai ci gaba da samun lada matukar ana ci gaba da amfani da rijiyar. Wato ba ya ga daukaka da ya samu a nan duniya saboda kafofin yada labarai sun yada shi, inda mai yiwuwa ma a samu wani ya gina masa gidan, saboda na ji labarin wadansu fitattaun mutanen sun ce za su kai masa ziyara har kauyen nasu. Haka kuma zai samu wata daukakar a Lahira saboda wannan sadaukarwar da ya yi domin amfanin jama’a. Wato lamarin nasa ya zama ‘ga lada ga la’ada’ ke nan. Allah Ya sa mu dace.
Ya kamata wannan ya zama darasi ga kowa cewa alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza. Shi kansa Malam Musa bai san cewa wannan abin da ya yi zai jawo masa daukaka a duniya ba, amma da yake ya yi da zuciya daya ne, saboda Allah, sai Allah Ya daukaka shi.
Haka kuma lamarin Musa ya kara nuna cewa gaskiya dokin karfe ce duk wanda ya hau ba zai yi nadama ba, gaskiya da rikon amana da ya nuna a yayin da yake aiki ne suka jawo wa Malam Musa daukaka. Haka nan yake har yanzu duk wanda ya kula da aikinsa kowane iri ne, ya yi shi da kyau ba ha’inci, to shi ma kuwa zai ga da kyau a karshen rayuwarsa. Allah Ya kara mana irin su Malam Musa Usman wadanda ke fifita ci gaban mutanensu fiye da son zuciyarsu.