✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna jiran hujjar Ortom cewa Fulani sun kai mishi hari —Matasan Arewa

Gamayyar Matasan Arewa sun nemi Gwamnan Binuwai ya kawo hujjar zargin da ya yi cewa Fulani sun kai masa hari.

Matasan Arewacin Najeriya sun kalubalanci Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwai ya kawo shaidar da ke tabbatar da zargin da ya yi cewa Fulani makiyaya ne suka kai masa hari.

A ranar Asabar ce ’yan bindiga suka bude wa ayarin motocin Ortom wuta a lokacin da yake dawowa daga gonarsa a hanyar zuwa Makurdi.

A jawabinsa ga ’yan jarida bayan harin, Ortom ya bayyana cewa Fulani makiyaya ne suka kai masa harin.

Gwamnan ya yi zargin cewa kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta yi barazanar kamo shi a raye, a taron da ta gudanar a Yola, Jihar Adamawa.

Amma Shugaban Gamayyar Matasan Arewa (AYF), Adamu Kabir Matazu, ya bayyana mamakin yadda har Ortom ya kai ga yin furucin ba tare da hujjoji ba.

“Mun ga an kai hari wa gwamnoni irinsu Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno, wanda aka bayyana hujjoji.

“Amma Ortom bai kawo hujjoji ba. Daga kowane bangaren al’umma akwai bata-gari, amma babu wata hujja da ke nuna cewa Fulani makiyaya ne suka kai masa hari,” inji shi.