Hukumar Sadarwa Ta kasa (NCC) ta bukaci al’ummar da ke hulda da kamfanonin sadarwa a kasar nan da su kwantar da hankulansu don tana bin hanyoyin da suka kamata wajen ganin kamfanonin ba sa cire musu kudi ba bisa ka’ida ba a duk lokacin da suka yi kiran waya ko karbar wani sako.
Shugabar Sashen Hulda da Jama’a Na NCC Misis Helen Obi ce ta bayyana haka a taron ganawa da al’umma (CCP) da hukumar ta shirya karo na 8 a Unguwar Lugbe da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ta ce NCC tana kula da yadda kamfanonin sadarwar ke cazar al’umma kudi don ganin ba a yin kuskure wajen cire wa al’umma kudi babu gairba, babu dalili.
“Hukumar NCC ta bullo da tsarin cazar al’umma kudi irin na bai daya a yayin kiran layi ko karbar sako kuma tuni ta sanar da kamfanonin sadarwa a game da hakan.. An yi haka ne don ganin kamfanonin ba sa wuce gona da iri a duk lokacin da suke cire wa al’umma kudi. A kan haka NCC ta kirkiro da sashen da ke lura da yadda kamfanonin sadarwar ke cazar al’umma kudi idan sun yi kira ko sun karbi wani sako don ganin ana bin tsarin sau da kafa ba tare da cuta ko cutarwa ba”.
“Kafin wani kamfanin sadarwa ya caji wani ko wasu kudin kira, tilas ne ya tuntubi Hukumar NCC kuma dole ne ya bi ka’idojin da muka shinfida game da hakan, kuma duk kamfanin da bai bi wannan ka’ida ba, to zai iya fuskantar hukunci. Wayar da kan kwastomomi yana da matukar muhimmanci, don haka ne muka yi wa taronnu na bana taken “Shekarar masu amfani da layukan sadarwa”.
Misis Obi sai ta yi kira ga al’umma da su rika amfani da lambobin “2442” ko “STOP” don su daina karbar irin sakonnin da ba sa bukata a kowane lokaci, ko kuma sakon “HELP” a duk lokacin da suka fuskanci wata matsala.
Ta ce idan al’umma suka yi amfani da lambobin da aka sanar amma duk da haka kamfanonin sadarwar ba su dauki wani mataki ba, ko kuma sun dauki matakin amma kwastomomin ba su gamsu ba, to suna iya kiran layin ‘622’ da Hukumar NCC ta kebe don a share musu hawaye, kuma kyauta ake kiran layin.
A nata jawabin tun da farko, Shugaban Sakandaren Gwamnati Ta Lugbe (Gobernment Secondary School Lugbe) Mista Gilla John ya yaba wa Hukumar NCC game da yadda take kai ziyara kowane sako da lungu na kasar nan da hakan ya sa al’umma suke samun damar bayyana matsalolin da suke fuskanta daga wajen kamfanonin sadarwa a kasar nan.
A nasa jawabin Hakimin Lugbe Mista Salisu Gode ya ce ya gamsu da irin tamboyin da al’ummarsa suka yi wa Hukumar NCC a lokacin da hukumar ta ziyarci yankinsa kuma ya gamsu da irin amsoshin da NCC din ta bayar.
Wannan taro daya ne daga cikin irin tarurrukan da Hukumar NCC ke yi a wurare da dama a fadin kasar nan. Kawo yanzu NCC ta ziyarci garuruwan Minna da Jos da Lakwaja da Makurdi da Suleja da Manda da kuma Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja kuma ana sa ran NCC za ta ci gaba da gudanar da irin wadannan tarurruka a sauran sassan kasar nan.